Sheikh Naim: Hizbullah Ba Za Ta Kwance Damarar Makamanta Ba

Sakatare-Janar na Hezbollah ya sake jaddada gargadi kan hankron  Isra’ila na ganin an kwance damarar kungiyar kamar yadda Amurkake jagorantar wannan yunkuri a kasar Lebanon.

Sakatare-Janar na Hezbollah ya sake jaddada gargadi kan hankron  Isra’ila na ganin an kwance damarar kungiyar kamar yadda Amurkake jagorantar wannan yunkuri a kasar Lebanon.

Gwagwarmaya dai za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka duk da matsin lamba da take fuskanta, in ji Sakatare-Janar na Hizbullah Naim Qassem, yana mai nanata cewa, barazana daga waje ko yunkurin tilasta musu aiwatar da wata ajanda da ta yi hannun rigada maslahar Lebanon ba zai hana su yin tsayin daka a kan matsayarsu  ba.

Sheikh Qassem ya tabbatar da cewa, Makiya suna shiri dare da rana domin ganin bayan gwagwarmayar al’ummar Lebanon, amma su kwana dasanin cewa, ba za mu taba ja da baya ba, ba za mu mika wuya ba, kuma za mu kare hakkinmu ko ta wane irin hali ne,” yana mai jaddada cewa matsayarsu tana tattare ne da akidarsu.

Ya kuma jaddada cewa, kungiyar Hizbullah ta kuduri aniyar kare hakki da muradun kasar Lebanon, kuma za ta ci gaba da aiwatar da manufofinta, ba tare da la’akari da kalubale ko jinkiri ba.

Ya kara da cewa, ba a bukatar ‘yan gwagwarmaya ko kasar Lebanon su dauki wani mataki kafin “Isra’ila” ta aiwatar da wani bangare na yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Ya ce  wasu na son Sojojin Lebanon su dauki matakin yin fito na fito da ‘yan kasarsu, amma masu wannan fata sun kare da bakin ciki, domin kuwa sun ga irin gagarumin hadin kai da ke akwai a tsakanin Sojoji da ‘yan gwagwarmaya.

Sheikh Naim Qassem ya jaddada cewa, bukatun gaggawa a yau sun hada da dakatar da wuce gona da iri ta kasa, da ruwa da kuma ta sama, da aiwatar da janyewar sojojin mamaya na Isra’ila gaba daya, da sakin fursunonin Lebanon, da sake gina kudancin Lebanon.

Ya kara da cewa “Idan aka kawar da kudancin Lebanon , to babu wata kasar Lebanon da ta rage, don haka dukkan ‘yan kasar ne ke da alhakin kare ta.”

Da yake yin tsokaci kan yarjejeniyar da aka cimma sama da shekara guda da ta gabata, Sheikh Qassem ya ce bangaren  Lebanon ya sha yin sassauci da saryar dawasu hakkoki, yayin da makiya Isra’ila ba su daina keta hurumin wannan yarjejeniya  ba.

Ya sake jadda cewa, ‘yan gwagwarmaya sun amince da alkawuran da suka dauka, sannan kuma kasar Labanon ta yi na’am da tanade-tanaden yarjejeniyar, amma duk da haka “Isra’ila” ta ci gaba da keta hurumin ta da kuma ci gaba da kutsawa cikin kasar ta Lebanon, yana mai tambaya, “Mene ne matsayin kasar game da sace jami’I Ahmed Shukr da aka yi a cikin kwanakin nan a yankin Zahle?”

Sheikh Qassem ya kara da cewa, “Kada ku kara neman wani abu daga gare mu” tare da gargadin cewa kada gwamnatin kasar ta bari ta  koma mai kare manufofin Isra’ila a sane ko a jahilce.

Sheikh Qassem ya bayyana Lebanon a matsayin wurin da ya tsonewa makiya ido,  yana mai jaddada cewa Amurka da  Isra’ila ne ke da alhakin farko kan rikice-rikice da kasar ke fuskanta.

Ya bayyana cewa kasar Lebanon tana gaban wani muhimmin mataki na tarihi da zabi guda biyu: na farko ta mika kai ga bukatun Amurka da “Isra’ila” wanda shi ne digon dan ba na wargajewar kasar, yayin da na biyu shi ne farfado da kasar da maido da ikonta ta hanyar takawa Isra’ila burki da hana aiwatardamanufofinta a kan kasar.

Jagoran na Hizbullah  ya bayyana gamsuwar kungiyar kan bin tafarkin  ‘yanci a matsayinta na  kungiyar Gwagwarmaya, yana mai tabbatar da cewa za ta ci gaba da kasancewa mai karfi, alfahari da jajircewa, komai sadaukarwa.

A cikin wannan yanayi, Sheikh Qassem ya tabbatar da cewa kwance damarar kungiyar  wani shiri ne na Amurka da Isra’ila,  kuma a yanzu an gabatar da shi ne a karkashin kebance ikon mallakar makamai ga gwamnati kadai, wanda hakan ba shi da wata ma’ana idan aka yi la’akari da ci gaba da kai munanan hare-haren Isra’ila a Lebanon, kuma wannan wani bangare ne na wannan aikin da muka ambata. In ji shi.

Ya kara da cewa, kawo batun makamai tare da ci gaba da kai hare-hare na Isra’ila yana biyan muradun “Isra’ila” da Amurka ne kai tsaye na kokarin raunana kasar Lebanon, ta yadda ba za ta taba zama mai ‘yancin tsayuwa kan kafafunta ko kare kanta ba.

Ya bayyana yadda aikin ke da nufin wargaza karfin soji na Lebanon, da haifar da sabani tsakanin Hizbullah da kungiyar Amal, da haifar da fitina tsakanin gwagwarmaya  da jama’a, ta yadda hakan zai baiwa Isra’ila damar cin karenta babu babbaka a cikin Lebanon da kuma ci gaba da mamayar yankunan kasar ba tare da wani ya daga mata kara ba.

“Dole ne makiya su aiwatar da yarjejeniyar tare da dakatar da keta ta; a lokacin  ne kawai za mu iya tattauna dabarun tsaron kasa da ke biyan muradun Lebanon.”  Inji Babban sakataren kungiyar Hizbullah.

Sheikh Qassem ya tabbatar da cewa kamar ko da yaushe kungiyar tana jin cewa nauyi da ya rataya a kanta ta yi duk abin da za ta iya yi domin al’ummar Lebanon su rayu a cikin ‘yanci da karama da daukaka da mutunci, ko da kuwa hakan zai kai su ga yin babbar sadaukarwa ta rayuwa da duk abin da suka mallaka a wannan duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted