Sheikh Na’im Kassim:  HKI Ta Keta Tsagaita Wuta Sau 60

Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya ce, Sau 60 HKI ta keta yarjejeniyar tsagaita wutar yaki,don haka nauyi ne a wuyan gwamnatin kasar

Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya ce, Sau 60 HKI ta keta yarjejeniyar tsagaita wutar yaki,don haka nauyi ne a wuyan gwamnatin kasar da kuma kwamitin sanya idanu da su tabbatar da kawo karshen hakan.

Sheik Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi dazu, ya kuma ce, kungiyar ta Hizbullah  wacce ta fuskanci mawuyacin hali, za ta sake farfadowa da karfinta.

Haka nan kuma Sheikh Na’im Kassim ya jinjinawa wadanda aka rushewa gidaje a kudancin Lebanon wadanda ya ce, su ne mutane mafi daukaka da daraja saboda yadda suke sadaukar da kai.

Babban magatarkar da kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce: Kowane wata za a bai wa duk wanda aka rusawa gida baki daya dala 500 har tsawon shekara daya kafin a gina masa gidan da aka rusa.

Wanda kuma gidansa rabi ne aka rushe za a ba shi dala 4000 a shekara daya, har a  gyara masa gidansa.

Danagen da abinda yake faruwa a Syria, Sheikh Na’im Kassim ya ce; Abinda yake faruwa aikin Amurka ne da Isra’ila, amma ba za su cimma manufarsu ba.

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma yi kira ga kasashen musulmi da su kawo karshen abinda yake faruwa a Falasdinu da kuma Syria.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments