Sheikh Kassim Ya Yi Kira Da A Bai Wa Sojojin Kasar Lebanon Makamai

Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheik Na’ima Kassim ya yi kira da a bai wa sojojin kasar makamai, sannan kuma a gudanar da

jagoran Hizbullah

Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheik Na’ima Kassim ya yi kira da a bai wa sojojin kasar makamai, sannan kuma a gudanar da zabuka a lokacinsu.

Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi na tunawa da shahadar Shahid Kassim Sulaimani da kuma  Injiniya Abu Mahdi a jiya da marece a birnin Beirut ya bayyana cewa;shahidan biyu sun kasance abin koyi a fagen aiwatar da musulunci da kuma ‘yan’adamtaka.

Haka nan kuma ya ce,Shahid Kassim Sulaimani ya kasance mai taimakawa gwgawarmayar musulunci da kuma dakile shirye-shiryen Amurka.

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah  ya kuma yi Ishara da yadda jamhuriyar musulunci ta Iran ta kasance a gaba wajen taimaka wa gwagwarmaya a Falasdinu domin fuskantar abokan gaba.

Sheikh Na’im ya kuma yi nuni da yadda kasar Lebanon take a matsayin abin kafa misali a fagen sadaukar da kai da daukaka da ‘yanto da kasa saboda hadin kai a tsakanin ‘yan gwagwarmaya, al’umma da kuma sojoji.

Bugu da kari Sheikh Na’ima Kasim ya yi jinjina ga al’ummun kasashen Yemen da Iraki da su ka kai wa Falasdinu dauki a lokacin yaki.

Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce yin shahada ba ya nufin samun tsaiko akan tafarkin gwgawarmaya, yana kara karfafata ne fiye da baya.

Akan siyasar kasar Lebanon, babban magatakardar kasar ta Lebanon ya yi kira da a gudanar da zabe a lokacin da aka tsayar ba tare da wani jinkiri ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted