Sharhin Bayan Labarai: Taron Tsaro Na Kasashe 4

Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da taron manya manyan kasashen yammacin Asia guda hudu a birnin Tehran, dangane da

Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da taron manya manyan kasashen yammacin Asia guda hudu a birnin Tehran, dangane da matsalolin tsaro a yankin, wanda ni tahir amin zan karanta.

///.. Madalla, a ranar litinin 26 ga watan Octoba da muke ciki ne, wakilan kasashen Saudia, Turkiyya Pakistan da kuma Iran suka gudanar da taro na musamman inda suka tattauna manya manyan matsalolin tsaron da yankin ya fada ciki tu bayan farwa kasar Iran da yaki, wanda Amurka da HKI suka suka yi a ranar 28 ga watan Fabrayru na wannan shekarar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a jawabin bayan taron kasashen guda hudu sun bayyana cewa zasu ci gaba da tattaunwa kan wannan matsalar a nan gaba ma, saboda muhimmancinsa har zuwa lokacinda aka warware matsalar ko matsalolin.

Janar Mohsen Rizaei sakaren majalisar koli na tsaron kasar Iran ne, ya karbi bakoncin sauran wakilan kasashen guda 3, wadanda suka hada da Yerima Khalid bin Salman ministan tsaron kasar Saudia, da Fiel Mashal Asim Munir babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Pakistan da kuma shugaban hukumar leken asiri na kasar Turkiyya Ibrahim Kalin.

Tattaunawar dai ta maida hankali ne kacokam kan yadda za’a dawo da zaman lafiya a yankin yammacin Asiya. Banda yakin da Amurka da HKI suka farwa kasar Iran da shi a farkon wannan shekarar, a cikin watan Yuli ne, wani sabon yaki ya sake barkewa tsakanin gwamnatin Ansarallah ta kasar Yemen da kasar saudia. Bayan da gwamnatin kasar Saudia ta hana wani jirgin fasinja na kasar Iran sauka a birnin San’aa babban birnin kasar Yemen. Wanda ya tilasta masa sauka a birnin Hudaida nab akin ruwa tekun Malia.

Daga nan ne gwamnatin kasar ta Yemen ta kaddamar da yaki da farko kan jiragen dakon man fetur na kasar saudia a takun Red sea, wadanda suke daukar man fetur daga tashar jiragen ruwa na Yanbu.

Sun haka jiragen saudia amfani da tekun malia da kuma mashigar ruwa ta babul Mandab. Sannan daga baya suka fara yaki gadan gadan da sojojin haya na kasar da saudia wadanda suke mamaye da kudancin kasar. Daga baya yakin ya fadada har zuwa lokacinda makaman kasar Yemen suka fara fadowa kan cibiyoyin man fetur na kamfanin Aramko na kasar Saudia da kuma tashoshin jiragen sama na kasar, wadanda suka hada da tashar jiragen sama na sarki Khalid dake birnin Riyad da na Dammam da Yanbu da sauransu.

Gwamnatin San’a dai tana bukatar Saudia ta kawo karshen takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa kasar tun shekaru kimani 12 da suka gabata, wato daga shekara ta 2015. Saudia ta samar da runduna ta kawayenta na kasashen larabawa har 10, don maida tsohon shugaban kasar ta Yemen Abdu rabbu hadi Mansur kan kujerar shugabancin kasar ta Yemen.

Bayan taron tsaro na Tehran a ranar Litinin sakaren majalisar koli na tsaron kasar Iran Janar Mohsen Rezaei ya gana da jakadan kasar Yemen a Tehran, inda bangarorin biyu suka tattauna kan taron kasashen hudu a Tehran da kuma abinda ya shafi yakin da ke faruwa tsakanin Saudia da kasar Yemen.

Taron tsaro na Tehran dai ya tattauna yanda kasashen yankin, ba tare da shigar kasashen waje cikin al-amuransu ba, su samar da tsaron yankin da kansu su kadai. Razaei ya fadawa jakadan kasar yemen a Tehran kan cewa, kasashen sun fara fahintar cewa babu zaman lafiya a yankin yammacin Asiya matukar Amurka ta ci gaba da samar da sansanonin sojojinta a cikin kasashen yankin.

Tun bayan farwa kasar Iran da yaki wanda Amurka da HKI suka yi a farkon wannan shekarar ne, sojojin Iran suka rufe mashigar ruwa ta Hurmuz, inda ta nan ne kashi kimani 20% da makamashi wadanda suka hada da man fetur da gas suke wucewa zuwa kasuwnanin duniya.

Rufe mashigar dai ya jawo matsalolin karancin makamashi a duk fadin duniya, sannan ya samar da matsalolin rayuwa a kasashen Amurka da Turai. Gwamnatin Amurka ta yi kokarin bude mashigar ruwa ta Hurmuz da karfin  soje amma sun kasa yin hakan. Masana suna ganin rufe mashigar ruwa ta harmus ya zama babban makamin Iran a yakin da take fafatawa da Amurka da kuma HKI tun kimani watanni 8 da suka gabata. Da alamun kuma , rufe mashigar zai yi tasiri a zaben yan majalisun dokokin Amurka wanda za’a gudanar a ranar 3 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted