Sharhi : Jawabin Shugaba Pezeshkian A Taron D-8 Karo Na 11″

A ranar Alhamsi ne aka gudanar da taron kungiyar kasshen musulmi masu tasowa wato D-8 karo na 11 a birnin Alkahira na kasar Masar, kuma

A ranar Alhamsi ne aka gudanar da taron kungiyar kasshen musulmi masu tasowa wato D-8 karo na 11 a birnin Alkahira na kasar Masar, kuma shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya na daga cikin shuwagabannin kasashen kungiyar da suka sami halattan taron.

Masoud Pezeskiyan shugaban kasar Iran a jawabinda ya gabatar a safiyar Alhamis a taron kungiyar na 11TH ya bayyana cewa, kasarsa a shirye take ta gina harsashe na samar da Bankin D-8 saboda ci gaban kasashe mambobi a cikinta.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana muhimmancin aiki tare na kasashen kungiyar don bunkasa tattalin arzikinsu, ya kuma yi kira ga kasashen su yi aiki tare a bangarori daban-daban don kara saurin bunkata tattalin arkin kasashen. Musamman a dai-dai lokacinda kasar Masar take jagorantar kungiyar, a jagorancin karba-karba.

Shugaban yace yana fatan kasar Masar zata yi kokarin ta samar da ci gaban a zo a gani a lokacinda take jagorancin kungiyar da kuma aiki tare a bangarori daban daban a cikin kasashe mambobi a cikinta.

Dangane da matsalolin tsaro a yankin gabas ta tsakiya kuma, shugaban ya yi allawadai da yakin da HKI taje jagoranta a Gaza, fiye da watanni 14 da suka gabata, da kuma abinda take yi na mamayar karin yankuna a kasar Siriya da kuma hare-haren da take kaiwa kasashen Lebanon da kuma Yemen.

Ya ce, sojojin gwamnatin HKI suna ci gaba da kissan falasdinawa maza da mata da yara, wadanda yawansu a halin yanzu ya wuce 45,000. Kuma mafi yawan wadanda suka kashe kuma suke ci gaba da kashewa mata da yara ne, wadanda basa dauke da makami.

Shugaban wa wani wuri a jawabinda ya ce, abinda HKI take yi a gaza ya sabawa dukkan dokokin kasa da kasa da suka hana irin wannan kissan kare dangi. Sannan ya bukaci hadin kan kasashen musulmi don fuskantar wadannan ayyukan ta’addanci wanda HKI da kawayenta Amurka da kasashen yamma suke tallafawa. Yace, hadin kan musulmi ne kawai zai iya kawo karshen halin da wasu kasashe a yankin suke ciki.

Har’ila yau a wani bangare na jawabinda shugaba Pezeshkiyan ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen na D-8 su kafa asusun ci gaba na kungiyar wanda zai tara kudaden jari na ko wace kasa daga cikin kasashen kungiyar, wanda kuma zai zama ginshikin harkokin kasuwanci tsakanin kasashen 8.

Yace kasar Iran , a namma a shirye take ta jagoranci kafa wannan asusun ta zaba jari da kuma kungiyar ta D-8. Yace kungiyar D-8 wata babbar kasuwa ce ga kasashen kungiyar, don haka wata dama ce ta habaka tattalin arzikin kasashen gaba daya.

Daga karshe ya tunatar da shuwagabannin kasashen kungiyar da kuma wakilansu kan cewa, cika alkawali yana da matukar muhimmanci a musulunci, don haka yakata duk abinda kungiyar ta amince ta kuma tsaya a kai, to a tabbatar da cika alkawari an kuma aiwatar da shi kamar yadda ya dace.

Babban sakataren kungiyar farfesa Abdulkadir Imam, a maida martani ga shawarorin da shugaba Masoud Pezeskiya na JMI ya gabatar, ya gede masa., ya kuma yi fatan, sauran kasashen kungiyar zasu taimaka don ganin an tabbatar da wadannan shawarori.

Sannan ya yabawa JMI kan irin rawar da take takawa a ci gaban kungiyar tun lokacin kafata ya zuwa yanzu. Ya yi kira ga kasashen kungiyar su amfani da irin ci gaban da kasar Iran take da shi a bangarorin ilmi da dama. Ya bukaci yan kasuwan kasar Iran su yi amfani da wannan damar don samun kasuwa a cikin mutane kimani biliyon 1.2 da kungiyar take da su.

A ziyarar da ya kai birnin Alkahira na kasar Masar, don halattan taron na D-8 shugaban Pezeskiyan ya hadu da shuwagabanni da kuma manya-manyan jami’an gwamnatocin sauran kasashen kungiyar.

Banda haka ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar ta D-8 wanda aka gudanar a birnin na Al-kahira kwana guda kfin taron shuwagabannin kasashen.

Shi ma a ganawarsa da tokwarorinsa na kasashen kungiyar Abbas Aragchi ya gana da Hakan Fidan ministan harkokin wajen kasar Turkiyya, inda suka tattauna sabban al-amura da suke faruwa a yankin Asia ta kudu, tare da maida hankali kan abubuwan da suke faruwa a kasar Siriya da kuma halin da ake ciki a Gaza.

Manya-manyan Jami’an diblomasiyyar kasashen  biyu sun jaddada bukata da kuma muhimmancin manya –manyan kasashen musulmi musamman kasashen D-8 na hada karfi da karfe don kawo karshen ta’asan da HKI take aikatawa a cikin kasashen musulmi, musamman a zirin gaza, Lebanon da kuma Siriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments