Sharhin Bayan Labarai Dangane Da Ganawar Islami Da Gorossi Na Hukumar IAEA A Vienna

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka ‘sharhin bayan labarai na yau zai yi magana dangane kekyawar niyyar JMI na aiki tare hukumar mai kula

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka ‘sharhin bayan labarai na yau zai yi magana dangane kekyawar niyyar JMI na aiki tare hukumar mai kula al-amuran makamashin nukliya ta duniya wato IAEA.

Mataimakin shugaban kasar Iran kuma shugaban hukumar makamashin nukliya ta kasar ya gana da shugaban hukumar makamashin Nukliya ta duniya Rafael Grossi a birnin Vienna inda ake taron gwamnonin hukumar karo na 68.

A ganawar dai Muhammad Islamu shugaban hukumar makamashin nukliya ta Iran ya bayyana cewa Iran zata ci gaba da kyautata dangantakar ta da hukumar IAEA matukar zata amfana da kasancewarta tare da ita.

Ita hukumar IAEA dai hukuma ce wacce MDD ta dorawa alhakin kula da al-amuran makamashin nukliya a duniya, da kuma sanya ida a kan ayyukan da kasashe mambobi a hukumar suke gudanarwa a kasashensu da suka shafi makamashin Nukliya, amma danganta tsakanin JMI ta Iran da hukumar tana rawa a mafi yawan lokuta saboda yadda hukumar take nuna bambanci a fili idan wani al-amarin da ya shafi shirin makamashin nukliya na kasar Iran na kuma zaman lafiya, ba na soje ba. Wannan kuma a fili yake kan cewa manya manyan kasashen duniya ko muce kasashen yamma musamman kasashen Amurka da Turai da kuma HKI suna shishigi cikin ayyukan hukumar, don ta takurawa JMI a shiryeshiryenta na makamashin Nukliya.

Don haka hukumar a mafi yawan lokuta takan bayyana cewa akwai sakku a cikin shirin makamashin nukliya na kasar Iran, sannan takan takurawa kasar Iran da manufar tilasta mata yin watsi da shirinta na makamashin nukliya gaba daya, wai don kada ta mallaka makaman Nukliya, wadanda da su ne manya manyan kasashen duniya masu kujerun na din din din a kwamitin tsaro na MDD suke gadara da shi. Da wadannan makaman ne suke tsorata kasashen duniya da dama, kan su yi biyayya a garesu ko kuma su fada cikin fushinsu.

Muhammad Islami shugaban hukumar makamashin Nukliya ta zaman lafiya na kasar Iran ya bayyana cewa, babu kasa wacce hukumar makamashin nukiya ta duniya IAEA take binciken ayyukanta a duniya a halin yanzu kamar jumhuriyar musulunci ta Iran. Wannan kuma yana faruwa ne saboda tasirin da kasashen yamma suke da shi a ayyukan hukumar. Sun maida hukumar a matsayin makama na yakar JMI.

Amma duk da haka, bai isheta ba, ko a taron gwamnonin hukumar karo na 67 da aka gudanar a birnin Vienna, sai da hukumar ta yi allawadai da JMI saboda wai tana boye wasu al-amura a cikin shirinta na makamashin nukliya.

Wannan tare da sanin cewa gwamnatin kasar Amurka ta fice daga yarjeniyar shirin Nukuliyar kasar Iran wanda aka fi sani da JCPOA a shekara ta 2018. Yarjeniya wacce kwamitin tsaro na MDD ta kafa kuduri mai lamaba 2231 don goyon bayan ta ta.

Amurka ta fice daga yarjeniyar wacce aka kullata a shekara ta 2015 tare da hujjan ita ce yarjeniya mafi munin wanda kasar Amurka ta taba amincewa da ita a tarihinta. Don haka shugaban kasar Amurka na lokacin ya sake dorawa JMI takunkuman tattalin arziki mafi muni a tarihin kasashen duniya, sannan tare da ita, kasashen Turai ma sun ki aikwatar da bangaren da ya zama wajibi a kansu na yarjeniyar ta JCPOA.

Sai duk da haka JMI ta ci gaba da kasancewa cikin yarjeniyar, bata yi watsi da shi ba har zuwa shekaru biyu da ficewar Amurka daga cikin yarjeniyar, wannan kamar yadda ita hukumar da kanta ta tabbatar a rahotannin da take bayarwa daga lokaci zuwa lokaci.

Sannan a lokacinda JMI ta maida martani ga Amurka da kuma turawan da suka ki aiwatar da abinda ya hau kansu a yarjeniyar ta JCPOA, ta rage wani abu daga cikin hadin kan da take bayarwa ga hukumar dangane da shirinta na makamashin nukliya. Kuma ta aiwatar da sabawarta da shirin na ta a cikin matakai daya bayan daya.

JMI ta rage hadin kan da take bawa hukumar IAEA a hankali ne don ta bawa wadannan kasashen, wato Amurka da Turai damar dawowa kan yarjeniyar ta JCPOA, ta kuma bayyana kekyawar aniyarta da hakan, amma har yau basu yi hakan ba.

Daga karshe JMI, duk tare da cewa ta yi watsi da wasu daga cikin hadin kan da take bawa hukumar IAEA a cikin shirinta na makamashi nukliya a bangare guda kuma ta na ayyukan bincike da samar da ilmi a fannin makamashin nuliya da sauri.

Wannan don nunawa kasashen yamma musamman kasar Amurka kan cewa Iran tana samun ci gaban da basa son ta samu a wannan fannin, kuma bata boyewa kowa.

A cikin taron hukumar ta IAEA karo na 68 a birnin Vienna hukumar Nukliya ta kasar Iran ta baje kolin irin ci gaban da ta samu a bangaren fasahar Nukliya ga kasashen kungiyar a cibiyar hukumar dake vienna.

Don haka a ganawar mataimakin shugaban kasar Iran kuma shugaban hukumar makamashin nukliya ta kasar Muhammad Islami da shugaban hukumar IAEA  Rafael Grossi, ya fada masa cewa Iran za ta ci gaba da karfin gaske wajen samar da ci gaba da ayyukan fasahar nukliya don tabbatar da cewa ta amfana kuma ta amfanar a wannan fanni mai muhimmanci ga rayuwar mutane a duniya a kuma wurare daban-daban.

Islami ya kammala da cewa ganawarsa, a ganawarsa da Gorossi ya nuna hukumar da kuma sauran kasashen duniya kan cewa Iran bata cikin matsaloli a cikin shirinta na makamashin nukliya na zaman lafiya. Kuma zata ci gaba da bincike da kuma gano irin amfanin da dan’adam zai samu a makamashin nukliya, ba sai an kai ga kera makaman nukliya mai kissan kare dangi ba.

A halin yanzu dai iran ta samar da magunguna da dama tare da amfani da makamashin nukliya a kasar Iran. Banda cibyar bada wutan lantarkin da take da shi a birni Bushar na kudancin kasar wacce take bada megawatt 1000 na wutan lantarki ga Iraniyawa, tana amfani da fasahar nukliya wajen ayyukan kiwon lafiya noma sararin samaniya da wasu wurare da dama. Masu sauraro karshen sharhin bayan labaran Kenan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments