Sharhin Bayan Labarai: Bunkasar Harkokin Kasuwanci Tsakanin JMI Da Rasha

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na ‘sharhin bayan labarai’ shiri wanda yake kawo maku karin bayana

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na ‘sharhin bayan labarai’ shiri wanda yake kawo maku karin bayana kan daya daga cikin labarai masu muhimmanci a wannan makon, da fatan masu sauraro za su kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///… Madallah masu sauraro shirimmu na yau zai yi Magana kan “Dangantakar tattalin arziki tsakanin JMI da kuma Rasah” musamman a cikin wannan lokacin da kasashen biyu suke fama da takunkuman tattalin arziki mafi muni daga kasashen yamma.

A makon da muke ciki ne shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa dangantakar tattalin arziki da kasuwanci tsakanin Rasha da JMI suna tafiyar kamar yadda ake so, kuma yana fatan zuwa karshen wannan shekara ta 2024 za su kara bunkasa, su habaka su kuma kara fadada.

Shugaban kasar ta Rasha ya bayyana haka ne a wani jawabin da ya gabatar a birnin Mosco a taron hannun jari na bankin VTB na kasar Rasha karo na 15.

Bankin VTB dai shi ne banki na biyu a girma a kasar Rasha, kuma yana daga cikin cibiyoyin kudi wadanda suke taka rawar a zo a gani, wajen bunkasa tattalin arzikin kasar Rasha da kuma fadada shi.

A wani wuri a maganarsa shugaban kasar ta Rasha ya bayyana cewa kasashen Rasha da JMI a matsayin kasashe makobta da juna, suna tafiyar da harkokin kasuwanci a tsakaninsu a fagage da dama, wadanda suka hada da makamashi, sifiri, masana’antu, gine-gine, ilmi da fasaha, masana’antun kayakin abinci, tsaron  da sauransu.

Shugaban ya kara da cewa, kasancewar kasashen biyu suna fama da takunkuman tattalin arziki mafi muni daga kasashen yamma, harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu zai bunkasar tattalin arziki su, kuma zai taimakawa kasashen biyu samun ci gaba a bangarorin daban-daban.

Kasashen biyu suna taimakawa juna wajen, cikata bukatun ko wanne daga cikinsu, musamman a bukatu wadanda kasashen yamma suka dora masu takunkuman tattalin arziki a kansu.

Shugaban ya ce, kasar Iran ta zama hanyar wucewar kayakin kasuwanci na kasar Rasha zuwa kasashen Asiya ta yamma da gabas, wato ‘transit’. kuma hanyar layin dogo wanda ake kira ‘hanyar Arewa zuwa Kudu’ ta na taka muhimmiyar rawa a cikin wannan shirin. Da wannan kuma kayakin kasuwanci na kasar Rasha suna iya wucewa zuwa, tashoshin jiragen ruwa na kasashen Pakistan da Indiya da sauran kasashen Asiya da sauri a cikin kuma farashi mai rahusa.

Shugaban ya kammala da cewa kasashen biyu, nan gaba kadan, idan shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya ziyarci kasar Rasha, zasu rattaba hannu kan yarjeniya ta musamman ta harkokin kasuwanci a tsakaninsu, kuma mai dogon zango. Idan haka ya faru, ana saran amfanin da kasashen biyu zasu samu a cikinta yana da yawa sosai.

Banda haka akwai fatan cewa hakan zai sassauta radadin takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma suka dorawa kasashen biyu.

A wani bangaren kuma, kasashen Rasha da JMI suna cikin kungiyoyin tattalin arziki na yankin da kuma na kasa da kasa wadanda suka hada da kungiyar tattalin arziki ta ‘Eurasia” da ‘Shanhaig’ ‘ECO’ da kuma BRICS.

Kasantowar kasashen biyu cikin wadannan manya-manyan kungiyoyin tattalin arziki a yankin da kuma duniya, zai taimaka sosai wajen sawwaka huldar kasuwanci mai yawa a tsakanin kasashen da kasashen kungiyoyin.

Don muhimmacin wadannan kungiyoyi, musamman kungiyar BROCS wanda kunshi kusan rabin mutanen duniya, zabebben shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta amincewa kungiyar BRICS ta kauracewa dalar Amurka a matsayin kudaden kasuwanci na kasa da kasa ba.

Ya zuwa yanzu dai wasu daga cikin kasashen kungiyar BRICS sun fara huldar kasuwanci a tsakaninsu, tare da mafani da kudaden kasashensu kai tsaye, ba tare da sanya dalar Amurka a tsakani ba.

Kungiyar BRICS dai tana son ganin ta samar da kudi na kanta wadanda zasu maye gurbin dalar Amurka a harkokin kasuwanci na kasa da kasa, akalla ko da a cikin kasashen kungiyar ne kadai.

Masu sauraro karshen sharhin bayan labaran Kenan.

=======================

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments