Bayan shafe kwanaki 470 na kisan kiyashi da Isra’ila ta yi a zirin Gaza, daga karshe an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kungiyar gwagwarmaya ta Hamas da gwamnatin Isra’ila, wadda ta fara aiki a ranar Lahadi.
Bayan sanarwar, Hamas ta ce yarjejeniyar ta samo asali ne sakamakon “jurewa na tsayin daka” da “juriya mai tsayi” na al’ummar zirin Gaza cikin sama da watanni 15.
“Yarjejeniyar kuma wata nasara ce ga al’ummar musulmi, da kuma kasashe masu ‘yanci in ji Hamas.
Tsakanin yammacin ranar Laraba, lokacin da aka cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta zuwa safiyar Lahadi, lokacin da yarjejeniyar ta fara aiki, hare-haren da Isra’ila ta kai a fadin Gaza, sun kashe Falasdinawa akalla 120, ciki har da mata 32 da kananan yara 30, tare da jikkata wasu 266, a cewar wata kididdiga ta hukumomin Gaza.
A cikin watanni 15 da suka gabata, tun daga watan Oktoban 2023, Isra’ila ta kashe mutane akalla 46, 800 tare da jikkata sama da 110,600.
Har ila yau gwamnatin ta fadada hare-haren kisan kiyashi zuwa kasashen Lebanon, Siriya da kuma Yemen a cikin wannan lokaci bayan ta kasa cimma wata manufa ta soji a Gaza.
Bayan shafe watanni 15 na yakin gwamnatin Tel Aviv ta kasa cimma muhimmiyar manufarta ta soja ta neman kawar da kungiyar Hamas da sauran kungiyoyin gwagwarmaya a Gaza.
Bari mu yi waiwaya baya na abubuwan da suka faru tun yakin na Isra’ila a Gaza.
Ranar 7 ga Oktoba, 2023 : kungiyar Hamas ta kaddamar da wani farmaki mai cike da tarihi kan yahudawan sahyuniya a matsayin mayar da martani ga mamayar da aka shafe shekaru da dama ana yi wa yankinsu.
Wannan farmakin da ba a taba yin irinsa ba ya girgiza gwamnatin Isra’ila da kuma masu mara mata baya daga kasashen yammacin duniya, lamarin da ya haifar da barna mai yawa.
Oktoba 17, 2023: Gwamnatin Isra’ila ta kai hari a asibitin Larabawa na Al-Ahli da ke birnin Gaza a wani kazamin hari na farko, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 500, akasari yara da mata.
Oktoba 27, 2023: Isra’ila ta ba da sanarwar mamaye Gaza. Ta hanyar kai Hare-haren ta sama, da farmaki ta kasa, da kuma korar Falasdinawa daga arewacin Gaza zuwa kudanc.
3 ga Nuwamba, 2023: Shugaban kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sayyed Hassan Nasrallah, a jawabinsa na farko bayan barkewar kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza ya ce Amurka ce ke da alhakin yakin da ake ci gaba da yi a Gaza da al’ummarta, inda ya bayyana Isra’ila a matsayin wani makamin kisa kawai. .”
4 ga Nuwamba, 2023: Sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza ya fuskanci hare-hare da dama da Isra’ila ta kai, wanda ya yi sanadin jikkatar mutane masu yawa, yawancinsu yara da mata.
11 ga Nuwamba, 2024: Wani hari da Isra’ila ta kai kan wani tanti da ke zaman mafaka a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat, ya kashe akalla mutane uku, ciki har da iyayen tagwaye ‘yan shekaru 10 da suka samu munanan raunuka. Kimanin wasu 24 kuma sun jikkata kuma an kai su Asibitin Awda da ke Nuseirat.
15 ga Nuwamba, 2023: Dakarun mamaya na Isra’ila sun shiga cikin babban asibitin, Al Shifa na Gaza, , bayan wani hari da aka shafe kwanaki da dama ana yi, inda jami’an kiwon lafiya suka bayar da rahoton cewa, marasa lafiya, ciki har da jariran da aka haifa, sun mutu sakamakon rashin wuta da kayan aiki.
Disamba 4, 2023: Dakarun mamaya na Isra’ila sun kaddamar da wani gagarumin farmaki na farko a kudancin Gaza, zuwa babban birnin Khan Younis.
2 ga Janairu, 2024: An kashe Saleh al-Arouri, mataimakin shugaban kungiyar gwagwarmaya ta Hamas da ke Gaza, a wani harin da jiragen yakin Isra’ila suka kai a yankin Dahiyeh da ke kudancin Beirut.
12 ga Janairu, 2024: Amurka da Birtaniya sun harba wasu jerin makamai masu linzami, kan Yemen don mayar da martani ga goyan bayan da al’ummar Yemen ke baiwa falasdinawa
Fabrairu 29, 2024: Fiye da Falasdinawa 100 ne aka kashe a wani hari da aka kai kan ayarin motocin agaji bayan da sojojin Isra’ila suka bude wuta kan jama’ar da suka taru a kusa da motocin agaji.
Afrilu 1, 2024: Harin Isra’ila ya kashe ma’aikatan hukumar Abinci ta Duniya bakwai da ke kai agaji a Gaza.
Mayu 2024: Gwamnatin Isra’ila ta ba da umarnin ficewa daga Rafah tare da kaddamar da hare-hare, tare da korar dubban daruruwan Falasdinawa.
Ta kai harin bam a sansanin Tel al-Sultan da ke Rafah, wanda aka kebe a matsayin wani yanki mai tsaro, tare da cinna wa sansanin wuta, tare da kashe Falasdinawa akalla 50.
Mayu 30, 2024: Amurka da Birtaniya sun kai wasu hare-hare ta sama a Sanaa da Hodeidah, na Yemen. Hare-haren sun kashe mutane 16 tare da jikkata 42.
Mayu 31, 2024: Sojojin Yaman sun kai hari da makami mai linzami kan wani jirgin ruwan Amurka da ke cikin tekun Bahar Maliya.
Harin dai ya zo ne a matsayin martani ga hare-haren da Amurka da Birtaniya suka kai kan lardin Hodeidah, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 16.
Yuni 2024: Isra’ila ta kai hari a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat a tsakiyar Gaza.
Daya daga cikin hare-haren ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa da dama bayan da ya auna wata makarantar da Majalisar Dinkin Duniya ke kula da ‘yan gudun hijira.
Bayan kwanaki biyu sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa 274 a daya daga cikin mafi munin kisan kiyashi.
Yuli 30, 2024: An kashe Fuad Shukr, wani babban kwamandan gwagwarmayar Hizbullah a wani harin da Isra’ila ta kai a yankunan kudancin Beirut.
Yuli 31, 2024: Gwamnatin Isra’ila ta kashe Ismail Haniyeh, shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas a Tehran.
Ya je kasar Iran ne domin halartar bikin rantsar da shugaba Masoud Pezeshkian.
Satumba 17, 2024: hare haren na’urorin sadarwa na hannu a Lebanon ya kashe akalla mutane 12 tare da raunata kusan 3,000.
Kasa da sa’o’i 24 da suka wuce, an samu irin wannan fashe fashen na na’urorin Walkie-talkie a fadin kasar, wanda kasashen duniya da dama sukayi Allah wadai da shi a matsayin wani babban ta’addanci da gwamnatin Isra’ila ta aikata.
20 ga Satumba, 2024: Isra’ila ta kashe Ibrahim Aqil, wani babban kwamandan kungiyar Hizbullah a wani harin da ta kai ta sama kan wani gida da ke unguwar Dahieh a birnin Beirut na kasar Lebanon.
Harin ya kashe akalla mutane 14 tare da jikkata wasu 66.
Satumba 27, 2024: An kashe Sayyid Hasan Nasrallah shugaban kungiyar Hizbullah a wani harin da Isra’ila ta kai a birnin Beirut na kasar Lebanon.
Harin dai ya hada da wasu hare-hare ta sama wanda ya lalata gine-gine da dama a yankunan kudancin birnin Beirut.
An kuma kashe Ali Karaki, babban kwamandan kungiyar Hizbullah, da Abbas Nilforoushan, babban mai ba da shawara kan harkokin soji na Iran, a wannan ta’addanci.
Satumba 29, 2024: Sojojin Yaman sun harba makami mai linzami kan filin jirgin sama na Ben Gurion, wanda ya girgiza gwamnatin kasar.
13 ga Oktoba, 2024: Hizbullah ta kai hari da jirage marasa matuka a barikin Zar’it na Golani Brigade da ke kusa da Binyamina. Harin ya kashe sojojin gwamnatin da dama.
Oktoba 16, 2024: Yahya Sinwar, fitaccen jagoran gwagwarmayar Hamas, sojojin mamaya na Isra’ila sun kashe shi a unguwar Tel al-Sultan da ke Rafah a kudancin zirin Gaza.
19 ga Oktoba, 2024: Hezbollah ta kai wani hari da jirgi mara matuki wanda ya auna gidan firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a Kaisariya.
12 ga Nuwamba, 2024: A daidai lokacin da ake cika kwanaki 40 da shahadar shugaban kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah, kungiyar Hizbullah ta kara kai hare-hare kan sansanonin sojan Isra’ila, ta hanyar amfani da jirage marasa matuka da makamai masu linzami iri-iri.
18 ga Nuwamba, 2024: Kungiyar gwagwarmaya ta Hezbollah ta kai hari kan wani gidan sirri na kwamandan rundunar sojin saman Isra’ila Manjo Janar Tomer Bar da ke Tel Aviv.
Nuwamba 22, 2024: Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ta bayar da sammacin kame Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da ministan harkokin soji na Isra’ila Yoav Gallant.
Nuwamba 27, 2024: Ministan harkokin wajen Qatar ya sanar da tsagaita wuta tsakanin gwamnatin Isra’ila da kungiyar Hizbullah ta Lebanon.
Disamba 31, 2024: Dakarun Yaman sun aiwatar da wani gagarumin farmaki da aka kai kan muhimman ababen more rayuwa na Isra’ila.
Janairu 11, 2025: Amurka, Birtaniya, da Isra’ila sun kaddamar da hare-hare a yankunan Yemen na Sana’a, Hudaydah, da Amran.
Janairu 15, 2025: Bayan kwanaki 470 na kisan kare dangi a zirin Gaza, yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Hamas da gwamnatin Isra’ila ta fara aiki da safiyar ranar Lahadi 19 ga watan janairu.
Ma’aikatar shari’a ta Isra’ila ta saki sunayen Falasɗinawa 95 da za a saki ranar Lahadi sakamakon aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.
A matakin farko na yarjejeniyar kuma Falasdinawa zasu saki wasu ‘yan Isra’ila guda uku a wannan Lahadin.
By Alireza Akbari