Sharhi: tattaunawa ta wayar tarho tsakanin Iran da saudiya.

shugaban kasar iran Masud pezeshkiyan a tattaunawa ta wayar tarho da yayi da shugaban kasar Saudiya mohammad bin salman ya fadi cewa mataken da iran

shugaban kasar iran Masud pezeshkiyan a tattaunawa ta wayar tarho da yayi da shugaban kasar Saudiya mohammad bin salman ya fadi cewa mataken da iran take dauka na hadin kai da hada kawukan alummomi da mazhabobi , a mataki na yankin da kuma kokarin karfafa dangantaka da  bunkasa huldar abokantaka da fadada hadin gwiwa da kasashen Musulmi tare da dogaro da hanyar ‘yan uwantaka ta Musulunci. lamarin babba kuma mai muhimmanci”

shugaban kasar iran ya fadi cewa bisa yin aiki tare zamu iya samar da yanki mai aminci, da samar da ci gaba da gina alummar mu,

haka zalika pizeshkiyan da yake jinjinawa irin goyon bayan da kasashen muslmi suke bawa alummar iran musamman ma daga bangaren kasar saudiya  yace barazana da yakin kwakwalwar da Amurka take yi don ta rikita zaman lafiya yankin ne,  kuma babu abin da hakan zai haifar face kawo rashin zaman da tsaro garesu,

Ana sa bangaren mohammad bin salman yarima mai jiran gadon na kasar saudiya ya fadi a lokacin tattaunawarsu ta wayar tarho da shugaban kasar iran cewa hadin kai tsakanin kasashen musulmi yana da matukar muhimmanci musamman ma a wanna yanayi da ake ciki.

tattaunawar wayar tarho tsakanin shugaban iran da mohammad bin salman ba wai tattaunawa ta wayar tarho ta diplomasiya ba ce kawai ,ana ganin wannan tattaunawar a matsayin wata alama ta sabuwar hanya mai karfi ta manufofin kasashen waje na jamhuriyar musulunci ta iran game da duniyar musulunci

iran bata daukar kanta a matsayin mai fafutukar siyasa kawai , a’a tana daukar kanta a matsayin memba babba ta kasashen musulmi wanda ke da alhaki na dabi’a da dabaru ga sauran kasashen musulmi, saboda haka hadin guiwa shi ma wata muhimmiyar bukata ce ta dabarun,

 wannan ra’ayin yana shimfida harsashin wani naui na asali da haduwa tare cikin dabaru a duniyar musulunci wanda zai iya taka rawa wajen daidaita matsin lamba da tsoma baki da ake fuskanta daga manyan kasashe na duniya

iran ta gabatar da kanta a matsayin wata babbar abokiyar hulda ta kasashen musulmi wajen gina  makoma ta daban ga yankin, inda aka maye gurabin  dabarun fadadawa da dabarun hadin guiwa,  da kuma duba fannoni  daban-daban na hadin guiwa tsakanin iran da saudiya wannan ya nuna cewa  alakar dake tsakani ta wuce hulda mai sauki tsakanin kasashen biyu, wadda zaa iya yin amfani da ita wajen canza tsarin tsaro, tattalin arziki da siyasa na yammacin asiya. dangantaka tsakanin Tehran da Riyadh tana shafar duniyar musulunci har ma da tsarin duniya.

A matsayin manyan kasashe biyu a yammacin asiya, iran da saudiya suna taka muhimmiyar rawa wajen tsara yanayin tsaro, siyasa da tattalin arziki na yankin, hadin guiwa tsakanin wadannan kasashen biyu, bayan dangantakar kasashen biyu, yana da sakamako mai yawa da kwanciyar hankali a yanki , yana rage tashin hankali na addini, yana dauke da tsoma bakin kasashen waje da ci gaban tattalin arziki,

kasar iran ta yi imanin cewa ci gaban yanki yana yiyuwa ne kawai ta hanyar hadin guiwa kuma wannan hanyar ta sanya iran a matsayin mai goyon bayan hadin gwiwa tsakanin kasashe da dama.

iran da saudiya muhimman kasashe ne a duniyar musulmi, hadin guiwa tsakanin wadannan kasashen biyu na iya yin tasiri kai tsaye ga tsaro, kwanciyar hankali da wadata a yankin, bangarorin biyu suna jaddada hadin kai na musuluci da kuma muradun kasashe, wannan haduwar na iya zama wani muhimmin ci gaba wajen samar da daidaiton siyasa a yammacin Asiya.

haduwar Tehran da Riyadh ba wai kwai bukata ce ta kasashen biyu ba kawai , A’a har ma da yankin baki daya, hadin guiwar siyasa tsakanin iran da saudiyya zaa iya dauka a matsayin wurin fara kafa tsarin tsaro na gida a yammacin asiya,  samar da tsari bisa tattaunawar hadin guiwa da kuma daukar nauyi tare.

hadin guiwa a fannin tattalin arziki tsakanin kasashen biyu na iya zama abin da ke haifar da ci gaba a yankin, iran da saudiya suna da manyan damarmaki na makamashi Albarkatun kasa, hadin guiwar wadannan karfin na iya haifar da kwanciyar hankali a kasuwar makamashi, habaka ayyukan hadin guiwa karuwar ciniki da karfafa hanyoyin sufuri a fadin yankin baki daya

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted