Sharhi : Matakin Iran na sake rufe mashigar ruwa ta Hormuz

Rundunar sojin Iran ta ce ta sake rufe mashigar Hormuz saboda ci gaba da toshe tasoshin ruwanta da Amurka ke ci gaba da yi. Kamfanin

Rundunar sojin Iran ta ce ta sake rufe mashigar Hormuz saboda ci gaba da toshe tasoshin ruwanta da Amurka ke ci gaba da yi.

Kamfanin dillancin labaran Fars da ke da alaka da dakarun juyin juya halin ƙasar, da kamfanin dillancin labarai na Iran Students da kuma kafar yada labarai ta kasar IRIB, sun rawaito wata sanarwa daga rundunar ta IRGC na cewa mashigin ruwan zai koma “irin yadda yake a baya”, inda dakarun da ke dauke da makamai suka mamaye yankin.

Sanarwar da sojojin ta fitar ta zargi Amurka da “fashin teku”, tana mai cewa “abin da Amurka ke yi” ya kai fashin teku.

Tun da farko Iran ta yi barazanar janye matakin da ta dauka na bude mashigar ga jiragen ruwa, matukar Amurka ba ta kawo karshen takunkumin hana jiragenta wucewa da ta sanya a tekun gabas ta tsakiya ba.

Sai dai Shugaba Donald Trump ya dage cewa matakin zai ci gaba da kasancewa har sai an cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya, yana gargaɗin cewa watakila ba zai sake tsawaita tsagaita wutar da ake ciki ba idan ta kare ranar Laraba.

Tun da farko dai Iran ta sanar da sake bude mashigar Hormuz zuwa ga jigilar kayayyaki ta kasuwanci, bayan aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon.

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya ayyana cewa za a ci gaba da zirga-zirgar jiragen ruwa ta hanyoyin da aka tsara da kuma wadanda aka riga aka tsara, karkashin kulawar hukumomin ruwan kasar.

Bayan kafa yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon, Iran ta sanar a ranar Juma’a, da sake bude mashigar Hormuz. 

Babban jami’in diflomasiyyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Abbas Araghchi, ya tabbatar da sake bude wannan muhimmin mashigar ruwa, wanda ya jaddada cewa ayyukan ruwa za su ci gaba da gudana lafiya a karkashin kulawar Iran.

“Bayan tsagaita wuta a Lebanon, an ayyana wucewar dukkan jiragen ruwa na kasuwanci ta mashigar Hormuz a bude har zuwa sauran yarjejeniyar tsagaita wuta, tare da hanyar da aka riga aka sanar da ita wadda Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa da Harkokin Ruwa ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran,” za ta tafiyar da in ji Abbas Araghchi.

An rufe mashigin ruwan ga jiragen ruwa da ke da alaka da abokan gaba—wato, na Amurka da Isra’ila—da kuma wadanda ke aiki tare da shi.

A cikin kwanaki 40 na yakin da Amurka da Isra’ila suka shelanta kan Iran, sojojin Iran sun nuna juriya mai ban mamaki, inda suka ƙaddamar da hare-hare kusan 100.

A ranar 8 ga Afrilu, Amurka ta amince da shawarar Iran mai matakai goma a hukumance a matsayin tushen tsagaita wuta na dindindin a yankin.

Ɗaya daga cikin sharuɗɗan da Tehran ta gindaya, kuma ta sake nanata ta hanyar shiga tsakani na Pakistan, shi ne tsagaita wuta a dukkan fannoni, ciki har da Lebanon.

Da farko Washington ta amince da shirin kafin ta soke shawararta bayan matsin lamba daga Isra’ila.

A wannan rana, gwamnatin Isra’ila ta kaddamar da mummunan hari a Lebanon, inda ta kashe mutane sama da 350.

A martanin da ta mayar, Iran ta yi gargadin cewa za ta iya janyewa daga tattaunawar Islamabad mai muhimmanci da aka yi a makon da ya gabata idan hare-haren ta’addancin da aka kai wa Lebanon ba su tsaya nan take ba.

Wannan gargadin ya sa Amurka ta matsa wa Isra’ila lamba ta bi umarnin.

A karshe, Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da tsagaita wutar a bainar jama’a ranar Alhamis da daddare a lokacin da yake jawabi a Fadar White House. Kuma bayan hakan Tsagaita wutar da aka yi a Lebanon ya fara aiki da tsakar dare.

A ci gaba da yunkurin kawo karshen yakin a yankin, Wata babbar tawagar Pakistan ta gana da jami’an Iran a wannan Alhamis, a Tehran.

A cewar wasu majiyoyi, ta na dauke da sako ne daga Amurka, yayin da ake ci gaba da kokarin shirya zagaye na biyu na tattaunawa tsakanin Tehran da Washington.

Zagayen tattaunawar farko, wanda aka gudanar a makon da ya gabata, ya kare ba tare da cimma wata matsaya ba, saboda buƙatun Washington da suka wuce gona da iri da kuma na son kai wadanda suka hana cimma duk wani sakamako mai ma’ana.

Ba a bayyana ranar da wurin da za a yi zagaye na gaba na tattaunawar ba tukuna.

Amma Babban hafsan sojojin Pakistan kuma firaministan Pakistan ya sanar a ranar Asabar cewa sun kammala ziyarar diflomasiyya daban-daban a matsayin wani bangare na ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.

Field Marshal Asim Munir, babban hafsan sojojin Pakistan, ya kammala ziyarar kwanaki uku a Iran, inda ya gana da manyan jami’ai.

Wadannan tattaunawar sun nuna yadda Pakistan ta “jajirce na samar da mafita… da kuma inanta zaman lafiya da kwanciyar hankali,” a cewar wata sanarwa ta rundunar sojin Pakistan.

Tattaunawa tsakanin Amurka da Iran za ta iya gudana a Pakistan a cikin kwanaki masu zuwa a cewar bayanai.

Field Marshal Munir ya gana da shugaban Iran Massoud Pezechkian, da Ministan Harkokin Wajen kasar Abbas Araghchi, da kuma shugaban majalisar dokoki, Mohammad Bagher Ghalibaf.

Shi ma a nasa bangaren, Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ya sanar a ranar Asabar cewa ya kammala rangadin diflomasiyya a kasashe uku – Saudiyya, Qatar, da Turkiyya – a matsayin wani bangare na kokarin kawo karshen yakin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Jamhuriyar Musulinci ta Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted