Search
Close this search box.

Shahadar Falasdinawa 17 Sakamakon Hare-Hare Sojojin Yahudawan Sahayoniyya A Gaza

Akalla Falasdinawa goma sha bakwai ne suka yi shahada sakamakon hare-haren ta’addanci da aka kai a tsakiyar Zirin Gaza da kuma kudancinsa A rana ta

Akalla Falasdinawa goma sha bakwai ne suka yi shahada sakamakon hare-haren ta’addanci da aka kai a tsakiyar Zirin Gaza da kuma kudancinsa

A rana ta 256 da fara kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar Falasdinu, sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun ci gaba da kai hare-hare a yankuna da dama na Zirin Gaza, da suka hada da tsakiyar birnin da kuma kudancinsa, lamarin da ya yi sanadin shahadar Falasdinawa akalla 17 tare da jikkatan wasu da dama.

Kamfanin dillancin labaran Falasdinu “Wafa” ya ruwaito cewa: Ma’aikatan bada agajin gaggawa sun gano gawarwakin shahidai 8 da wasu da dama da suka samu raunuka, sakamakon harin da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a wani gida na iyalan Al-Ra’iy, da kuma gawarwaki 5 na Falasdinawa da aka kashe su a gaban shagunansu daga iyalan Al-Madhoun da ke sansanin Nuseirat a tsakiyar Zirin Gaza, kuma an kwashe gawarwakin zuwa asibitin Al-Awda.

Har ila yau, jirgin saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi luguden wuta kan gidan iyalin Harb a sansanin Bureij, wanda ya yi sanadin shahada Falasdinawa masu yawa tare da raunata wasu na daban.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments