Ma’aikatar harkokin wajen kasar Senegal ta sanar da cewa hambararren shugaban kasar Guinea Bissau UOumar Sissoko Embalo ya isa kasar a cikin wani jirgin sama na musamman.
Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Senegal ta fitar a jiya Alhamis ta ce an dauko shi ne a cikin jirgin sama na musamman bayan da kungiyar tattalin arziki ta yammacin Afirka ( Ecowas) ta tsoma baki.
Juyin mulkin bayan nan da aka yi wanda ya hambarar da gwamantin Umar Sisoko shi ne na tara da aka yi a cikin shekaru biyar a wannan kasar.
Sojojin kasar sun sanar da ayyana Horta N’Tam a matsyain shugaban gwamnatin soja an kuma rantsar da shi.
Kungiyar raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta yi Allah wadai da juyin mulkin da na kasar Guniea Bissau, kwanaki uku bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu, inda ta kira shi da “barazana kai tsaye ga zaman lafiyar kasar da yankin.”
Wannan “juyin mulkin soja” ya zama “mummunan keta tsarin mulki” kuma “barazana kai tsaye ne ga zaman lafiyar kasar da yankin baki daya,” in ji ECOWAS a cikin wata sanarwa da ta fitar.
Dama kafin hakan Shugabannin tawagar masu sa ido kan zaben na Guinea Bissau na kungiyar Tarayyar Afirka da ECOWAS, sun bayyana ” matukar damuwa game da sanarwar da sojoji suka yi na yin juyin mulki a kasar.”
Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana bin diddigin lamarin da “matukar damuwa,” tana kira da a girmama bin doka.