Sayyid Muqtada Sadr Ya Bukaci Koran Jakadan Amurka Daga Kasar Iraki

Sayyid Muqtada Al-Sadr ya bukaci a koran jakadan Amurka da kuma rufe ofishin jakadancinta a birnin Bagadaza A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa

Sayyid Muqtada Al-Sadr ya bukaci a koran jakadan Amurka da kuma rufe ofishin jakadancinta a birnin Bagadaza

A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na twitter a yau Talata 28 ga watan Mayun shekara ta 2024, Sayyid Muqtada Al-Sadr ya bayyana al’ummar yahudawan Sahayoniyya a matsayin ‘yan ta’adda marasa kunya, masu kiyayya ga addinan da aka saukar daga sama, wadanda suke zubar da jinin dukkanin mabiya addinai cikin rashin kunya, yayin da ya yi nuni da cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila gwamnatin ‘yan ta’adda ne don haka bata dace da zama gwamnati ba.

Sayyid Al-Sadr ya bukaci a kori wadanda ya kira wawayen Amurkawa daga kasar Iraki, kuma a rufe ofishin jakadancinsu ta hanyar diflomasiyya ba tare da zubar da jini ba. Kamar yadda Malam Al-Sadr ya yi kira ga Kungiyar hadin kan kasashen musulmi da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa da su taka gagarumar rawar domin ganin kawo karshen kisan kiyashi da makiya yahudawan sahayoniyya suke kai wa al’ummar Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments