Jagoran kungiyar “Ansarullah” ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husi wanda ya gabatar da jawabi da a ciki ya yi bitar abubuwan da suke faruwa a cikin wannan yankin, ya bayyana cewa; A tsawon shekara daya sun kai hare-hare akan jiragen ruwa 211.
Shugaban kungiyar ta Ansarullah, ya kuma ce, jiragen Amurka suna gujewa bin ta hanyar da za su yi gaba da gaba da sojojin Yemen, sai suke boyewa a bayan jiragen ruwan China.
A jawabin da ya yi a yau Alhamis Sayyid Abdulmalik al-Husi ya ce; Kafafen watsa labarun duniya suna ganin yadda jiragen ruwan na Amurka suke boyewa a bayan jiragen ruwan China domin su sami kariyarsu.
Sayyid Abdulmalik Al-Husi ya kuma ce; Suna cigaba da farutar jiragen abokan gaba, da ya zuwa yanzu sun kai bara akan jiragen da adadinsu ya kai 211.
Har ila yau shugaban kungiyar ta Ansarullah ya kuma yi ishara akan nau’oin hare-haren da suke kai wa a kan teku da suke nufar jiragen ruwan Amurka, sai kuma wadanda suke kai wa a cikin HKI da suka hada da filin jiragen sama na Bin Gorion da kuma matsugunin ‘yan share wuri zauna na Askalan.