Sayyid Abdulmalik Husi: Taimakon Da Ake Jefawa Gaza Ta Sama Yaudara Ce

Shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik Al-Husi wanda ya gabatar da jawabi a jiya  Alhamis, ya bayyana abinda yake faruwa a Gaza da cewa, yana nuni

Shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik Al-Husi wanda ya gabatar da jawabi a jiya  Alhamis, ya bayyana abinda yake faruwa a Gaza da cewa, yana nuni da halayyar keta da mugunta ta ‘yan sahayoniya, don haka ya zama wajibi akan al’ummar musulmi da dukkanin jinsin bil’adama da su kalubalanci wannan irin zalunci da ba shi da tamka.

Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kuma ce, wadanda aka fi cuta a Gaza su ne kananan yara, sannan kuma ya yi ishara da yadda kasashen larabawa da kuma kungiyoyin kasa da kasa su ka kyale Gaza.

Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya ce; Da akwai kananan yara 100,000 da suke fuskantar hatsarin mutuwa saboda yunwa a Gaza, daga cikinsu da akwai jarirai 40,000 da suke fuskantar rashin madarar da za su sha.

Dangane da kayan abincin da ake jefawa ta sama a wasu sassa na Gaza, ya bayyana ta a matsayin yaudara sannan kuma tarko ne nak isa, domin ana kashe sui dan sun je daukar kayan abincin.

Haka nan kuma ya yi kira ga al’ummar Musulmi da larabawa da su kalubalanci wannan babban laifin da HKI take yi a cikin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments