Iran Ta Ce Batun Neman Dakatar Da Tace Uranium Zai Rusa Duk Wata Jarjejeniya Da Ake Son Cimmawa

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Matukar dai Trump ya bukaci dakatar da inganta sinadarin Uranium gaba daya a Iran, to ba za a cimma wata yarjejeniya ba Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Araqchi ya jaddada a wata hira da jaridar Financial Times cewa: Iran na neman a biya ta diyya kan […]
Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Watsi Da Duk Wani Zarge-Zargen Neman Bata Mata Suna

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta musanta zarge-zargen da Amurka da kasashen yamma suka yi mata Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Ismail Baqa’i ya musanta zarge-zargen da Amurka da Faransa da wasu kasashen yammacin Turai ke yi wa Iran a matsayin abin dariya da rashin tushe. Ya kuma jaddada cewa, suna daga cikin fito-na-fito na hasashe […]
Limamin Sallar Juma’a Ya Ce; Iran Zata Mayar Da Isra’ila Kufai Idan Ta Sake Kai Hari Kan Kasarta

Limamin da ya jagoranci sallar Juma’ar birnin Tehran ya bayyana cewa: Iran za ta mayar da birnin Tel Aviv kufai idan ta maimaita wautar ta Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, Ayatullah Ahmad Khatami, ya gargadi shugabannin yahudawan sahayoniyya kan illar duk wani keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta […]
Kasar Slovenia Da Haramta Tura Makamai Zuwa Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Slovenia ta kasance Ƙasar Turai ta farko da ta ba da sanarwar hana tura makamai zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila Kasar Slovenia ta sanar da haramta musayar zirga-zirgan kayayyakin kasuwanci tsakaninta da haramtacciyar kasar Isra’ila musamman safarar makamai da kayan aikin soji zuwa Isra’ila, inda ta zama kasa ta farko ta Turai da ta dauki wannan […]
Kasar Spain Ta Bayyana Abin Da Ke Faruwa A Gaza A Matsayin Abin Kunya Ga Bil’Adama

Kasar Spain ta bayyana abin da ke faruwa a Gaza a matsayin abin kunya ga bil’adama Ministan harkokin wajen kasar Spain José Manuel Albares ya yi kira ga mahukuntan Isra’ila a ranar Alhamis da su bude mashigar ruwa na dindindin domin ba da damar kai agajin jin kai zuwa zirin Gaza, yana mai gargadin cewa; […]
Iran ta yi watsi da zargin gwamnatocin turai na yunkurin kashe wasu mutane a kasashensu

Iran ta yi watsi da zarge-zargen marasa tushe balantana makama da kasashen yammacin duniya ke yi a kanta, kan cewa tana yunkurin kashe wasu mutane a cikin kasashensu. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya yi Allah wadai da ikirarin da ya kira na kin jinin Iran da Amurka da Canada da wasu kasashen […]
Mali da Rasha sun tattauna kan hadin gwiwar makamashi

Wakilan kasashen Mali da Rasha sun gudanar da taron farko na kwamitin hadin gwiwa na gwamnatocin kasashen biyu, karkashin jagorancin ministan tattalin arziki da kudi na kasar Mali Husseini Sanou, da ministan makamashi na kasar Rasha Sergey Tsivlev, inda suka tattauna kan “hadin gwiwa a fannin makamashi, musamman wajen yin amfani da makamashin nukiliya domin […]
Afirka ta Kudu na shirin daukar matakan kauce wa tasirin harajin Amurka

Ministan kasuwanci na Afirka ta Kudu Parks Tau ya fada jiya Alhamis cewa kasarsa na shirin yin shawarwarin kasuwanci da nufin kaucewa harajin kashi 30% na Amurka a kan kasarsa, wanda zai fara aiki daga wannan Juma’a. A farkon watan Mayu ne Afirka ta Kudu ta gabatar da wani shirin yarjejeniya ta kasuwanci ga gwamnatin […]
Haaretz: Sojojin Isra’ila 7 ne suka kashe kansu a watan Yuli

Gidan rediyon sojojin Isra’ila ya bayar da rahoto a wannan Alhamis cewa, wani soja ya kashe kansa bayan ya kwashe fiye da kwanaki 300 a cikin sojojin wucin gadi. Jaridar Haaretz ta Isra’ila ta bayar da rahoton cewa, adadin sojojin da suka kashe kansu a wannan watan kadai ya kai bakwai. A cikin wannan yanayi, […]
Gaza: Mutane Da Dama Sun Yi Shahada A Yau Wasu Kuma Sun Jikkata

Haramtacciyar kasar Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza a yau Juma’a, inda ta kai munanan hare-hare kan yankunan fararen hula da sansanonin ‘yan gudun hijira. Wadannan hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma jikkatar wasu a fadin yankin, lamarin da ke kara zurfafa damuwar da ake da ita […]
Kungiyar AU Ta Yi Watsi Da Kafa Gwamnatin Adawa Da Kungiyar RSF Ta Yi A Sudan

Jim kadan bayan da kungiyar kai Dauki Gaggawa ta kasar Sudan ta sanar kafa gwamnatin mai mambobi 15, kungiyar tarayyar Afirka ta mayar da martanin kin amincewa da ita. Bugu da kari kingiyar ta tarayyar Afirka ta kira yi kasashen da suke mambobi a cikinta da kuma kungiyoyin kasa da kasa da kar su amince […]
Shugaban Kasar Iran Zai Ziyarci Pakistan A Gobe Asabar

Kamfanin dillancin labarun ” Mehr” ya bayyana cewa; Ziyarar da shugaban kasar ta Iran zai kai zuwa Pakistan amsa karan Fira minister Shahbaz Sharif ne. Bugu da kari ziyarar za a yi ta ne a daidai lokacin da wannan yankin yake fama da sauye-sauye, haka nan kuma za ta mayar da hankali wajen bunkasa alakar […]
Habasha Ta Kaddamar Da Shirin Shuka Bishiyoyi Miliyan 700 A Rana Daya

A Alhamis din nan ne dai kasar ta Habasha ta fito da Shirin shuka bishiyoyi har miliyan 700 a rana daya, ta hanar shigar da miliyoyin mutanen kasar. Fira ministan kasar ta Habasha Abi Ahmad yana son a rika tunawa da shi anan gaba ta hanyar shuka bishiyoyin da za su kai biliyan 50, daga […]
Sayyid Abdulmalik Husi: Taimakon Da Ake Jefawa Gaza Ta Sama Yaudara Ce

Shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik Al-Husi wanda ya gabatar da jawabi a jiya Alhamis, ya bayyana abinda yake faruwa a Gaza da cewa, yana nuni da halayyar keta da mugunta ta ‘yan sahayoniya, don haka ya zama wajibi akan al’ummar musulmi da dukkanin jinsin bil’adama da su kalubalanci wannan irin zalunci da ba shi da […]