Shugabannin kasashen Afirka sun kammala taron kwanaki 3 kan sauyin yanayi na Afirka a babban birnin kasar Habasha a jiya Laraba tare da amincewa da sanarwar Addis Ababa, inda suka yi alkawarin mayar da nahiyar ta zama cibiyar samar da makamashi mai safta da kuma hanyoyin magance sauyin yanayi a yayin da suke neman kudade na gaske.
Shugaban kasar Habasha Taye Atske Selassie, wanda ya rufe taron, ya ce taron ya nuna cewa Afirka ba ta shiga cikin rikicin da ba ta haifar da shi ba.
” Mun himmatu wajen samar da wata nahiya mai wadata,” in ji shi.
“Zalunci ne cewa sama da ‘yan Afirka miliyan 600 har yanzu suna rayuwa ba tare da samun wutar lantarki ba.
Dole ne aikin mu na yanayi ya fara da saka hannun jari mai yawa don sabunta makamashi da kuma yin kira ga tabbatar da adalci.”
Taron na neman karfafa murya guda daya ta Afirka a fagen duniya kan rage illolin sauyin yanayi, tare da bunkasa tsare-tsaren da ke da amfani ga kasashen Afirka kafin taron COP da za a gudanar a Brazil a watan Nuwamba mai zuwa.
Bayar da kudi da tabbatar da adalci na yanayi a na daga cikin ajandar babban taron.
Bankin raya kasashen Afirka ya yi kiyasin cewa ana bukatar dala biliyan 100 a duk shekara domin daidaita ababen more rayuwa, da tsaron aikin gona, da zuba jari a fannin makamashin da ake iya sabuntawa a Afirka.
Sai dai a cewar wani rahoton sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya, dala biliyan 30 ne kawai aka tara wa Afirka tsakanin shekarar 2020 zuwa 2024 ta asusun kula da yanayi na Green Climate (GCF).
A cewar Mahamoud Ali Youssouf, shugaban hukumar ta AU, “kasashen Afirka na bukatar garanti mai karfi da sabbin hanyoyin samar da kudade don sauya burinsu zuwa ayyuka na zahiri.”
Bisa takardar share fagen taron, Afirka na bukatar kusan dala biliyan 579 don samar da kudaden da za ta samar da daidaita tsakanin shekarar 2020 zuwa 2030.