Shugaba Zelensky na Ukiraniya zai kai ziyara kasar Saudiyya a ranar Litinin, gabanin bude tattaunawar da za a yi tsakanin kasarsa da kuma Amurka da zummar kawo karshen yaki da Rasha.
Shugaban na kasar Ukiraniya ya wallafa wani sako a shafinsa na X cewa; Manufar ziyarar tashi ita ce haduwa da yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman, sannan kuma tawagar da zai je da ita, za ta ci gaba da zama a can Saudiyya din saboda yin aiki tare da mutanen Saudiyya da kuma Amurka.”
Zelensky ya kara da cewa; Kasarsa Ukiraniya tana son ganin an sami zaman lafiya mai dorewa.
Bugu da kari shugaban na kasar Ukiraniya ya ce; Matakin farko da kasarsa ta gabatar a matsayin shawarar kai wa ga zaman lafiya, shi ne dakatar da yaki a lokaci mafi kusa, da hakan zai zama share fage ne na warware sabanin da ake da shi baki daya,kuma Ukiraniya a shirye take ta yi aiki da Amurka a turai domin shimfida zaman lafiya”
Dangane da taron da za a yi a kasar Saudiyya, wani babban jami’in gwamnatin kasar ta Ukiraniya ya ce, a ranar Talata mai zuwa za a yi ganawa a tsakanin tawagar kasarsa da kuma ta Amurka a Saudiyya.
Jami’in na Ukiraniya ya ce ganawar za a yi ta ne a kokarin kyautata alaka a tsakanin kasashen biyu, bayan abinda ya faru na cacar baki a tsakanin Donald Trump a Zylenisky.
A gefe daya ministan tsaron Birtaniy John Healey ya furta cewa; Da akwai kyakkyawar dama ta tarihi domin shimfida zaman lafiya a Ukiraniya” sannan ya kara da cewa: “ Shugaban kasar Ukiraniya a shirye yake ya rattaba hannu akan yarjejeniya da Amurka, amma yana da bukatuwa da a ba shi lamuni.