Kasar Saudiyya ta sanar cewa za ta kara hannun jarinta a Amurka zuwa dala tiriliyan daya, daga dala biliyan 600 da kasar ta zuba a baya.
Yariman Saudiyyar ne Mohammed Ben Salman ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai tare da Shugaban Amurka Donald Trump a ziyarar da ya kai fadar gwamnatin Amurka, bayan ganawar sirri da suka yi.
A baya ne Trump ya bukaci Saudiyya da ta kara hannun jarinta a Amurka, sannan ya bukaci yariman ya tabbatar, inda shi kuma ya amsa da cewa, “tabbas.”
Shugaban na Amurka ya ce Saudiyya za ta zama “babbar kawar kawance wacce ba daga NATO ba,”
Ya kuma sanar da karfafa hadin gwiwar soja zuwa wani matsayi mafi girma ta hanyar ayyana Saudiyya a matsayin babbar kawar da ba ta NATO ba, wanda hakan wani abu ne mai matukar muhimmanci,” in ji Donald Trump.
Trump ya nanata wa bin Salam cewa yana “alfahari” da kasancewa abokinsa, sannan ya ƙara da cewa Amurka na “godiya da zuba jarin.”
Wannan na zuwa ne bayan Trump ya sanar a ranar Litinin cewa Amurka za ta sayar wa Saudiyya da jirgin yaƙin Amurka ƙirar F-35.
Wannan ce ziyarar bin Salman ta farko zuwa fadar gwamnatin Amurka tun a shekarar 2018, shekarar da aka aka kashe fitaccen dan jarida Jamal Khashoggi, wanda Trump ya bayyana a yanzu cewa mutum ne mai tsarkakiya sosai, amma MBS ya bayyana cewa an yi babban kuskure akan kisan nasa.
A watan Mayu ne Trump ya ziyarci Saudiya, inda kasashen biyu suka kulla yarjejeniyoyi da dama, wadanda Amurka ta ce sun kai na dala biliyan 456.