Sojojin Yemen Suna Da Makami Mai Linzami Da Babu Mai Makamancinsa Sai Iran

Wani masani harkar tsaro da dabarun yaki ya ce: Babu wata kasa a yankin da ke da makamai masu linzami irin na Yemen, sai kasar Iran kawai Kwararren mai kula da harkokin tsaro da dabarun yaƙi Laftanar Janar Abdul Karim Khalaf ya bayyana takamaiman makamin “Mayun” na Yemen, wanda aka sanya wa sunan ɗaya daga […]

Gwamnatin Mamayar Isra’ila Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta A Gaza Kusan Sau 400

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza kusan sau 400 Babban Daraktan Ofishin Yada Labarai na Gwamnati a Zirin Gaza, Ismail al-Thawabta, ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta aikata laifuka 393 da aka rubuta tun lokacin da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a Zirin Gaza. Ya jaddada cewa wadannan […]

Kasar Maziko Tayi Watsi Da Shirin Trump Na Kai Harin Soji Kan Iyakar Kasar.

Shugabar kasar maziko Claudia shinbaum ta fadi a cewa kasarta ta yi watsi da duk wani kokarin tsoma bakin kasashen wajen da kuma kalaman da shugaban Amurka Donald Trump yayi na kai harin soji kan iyakar kasar. A farkon makon nan ne trump yace yana so ya umarci sojoji su kaddamar da wani samame a […]

Iran : Dole ne kudirin Amurka ya kare hakkin Falasdinawa da samuwar kasar Falasdinu

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa dole ne kudirin Amurka da MDD ta amince da shi ya tabbatar da kare hakki da yancin Falasdinawa a sahun gaba samar da kasar Falasdinu. Jakadan Iran kuma wakilin dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeed Iraqini, ne ya bayyana haka, a matsayin martanin ga amincewar da kwamitin […]

Saudiyya za ta kara hannun jarinta a Amurka zuwa dala tiriliyan daya

Kasar Saudiyya ta sanar cewa za ta kara hannun jarinta a Amurka zuwa dala tiriliyan daya, daga dala biliyan 600 da kasar ta zuba a baya. Yariman Saudiyyar ne Mohammed Ben Salman ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai tare da Shugaban Amurka Donald Trump a ziyarar da ya kai fadar […]

Iraki : Jam’iyyar al-Soudani ta samu rinjaye a Majalisar dokoki

A Iraki an sanar da sakamakon karshe na zaben ‘yan majalisar dokoki da aka gudanar a ranar Talata data gabata. Sakamakon ya nuna cewa Jam’iyar Firaminista Mai Barin Gado Mohamed Shia al-Soudani ce ta sami rinjaye mai yawa a majalisar da kujeru 46, inda za ta rike kusan rabin kujerun, idan aka kwatanta da kasa […]

Shugaban gwamnatin Togo zai gana da Shugaba Putin na Rasha

A wani lokaci yau Laraba ne aka shirya shugaban majalisar dokokin Togo zai gana da Shugaban Rasha Vladimir Putin a Moscow. Tattaunawa tsakanin shugabannin biyu, wadanda suka dade suna da kyakkyawar dangantaka, za ta mayar da hankali kan zaman lafiya da tsaron yankin, da kuma batutuwa daban-daban, tun daga da makamashi zuwa ciniki da noma. […]