Saudiyya: Yemen Ta Kashe Mutane 17 A Filin Jirgin Sarki Khalid

Rundunar kawancen Larabawa karkashin jogorancin Saudiyya ta take yaki a Yemen ta ce: Mutane 17 sun mutu sannan 333 sun jikkata sakamakon hare-haren ‘yan Houthi

Rundunar kawancen Larabawa karkashin jogorancin Saudiyya ta take yaki a Yemen ta ce: Mutane 17 sun mutu sannan 333 sun jikkata sakamakon hare-haren ‘yan Houthi a filin jirgin saman Sarki Khalid

Kakakin rundunar kawancen da Saudiyya ke jagoranta, wacce ke goyon bayan gwamnati a Yemen, Manjo Janar Turki al-Maliki, ya sanar da cewa: Hare-haren da ‘yan kungiyar Ansarullahi ta Mabiya Houthi suka kai wa filin jirgin saman Sarki Khalid na kasar Saudiyya tsakanin 7 da 11 ga watan Oktoba sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 17 da kuma raunata mutane 333.

A yayin wani taron manema labarai da ya yi jawabi kan hare-haren da aka kai a filin jirgin da kuma ayyukan soji na rundunar, al-Maliki ya bayyana cewa an kai hare-hare sau 20 a filin jirgin saman Sarki Khalid tun daga ranar 1 ga Oktoba.

Al-Maliki ya dauki hare-haren da aka kai a filayen jiragen saman Masarautar Saudiyya a matsayin barazana ga tsaron yankin, yana mai kira ga ‘yan Houthi da su dakatar da abin da ya bayyana a matsayin ayyukan ta’addanci kan fararen hula nan take.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted