Makarantun suna daga cikin wuraren da Saudiyya ke kai musu hare-hare a kasar Yemen, inda a yanzu ta kaddamar da hare-hare kan cibiyoyin ilimi sama da 2,700
Wata kungiyar kare hakkin dan adam ta Yemen ta watsa rahoton hare-hare sama da 2,700 na Masaurautar Saudiyya ta kai kan cibiyoyin ilimi a kasar, yayin da hare-haren da ake kai wa makarantu ke kara ta’azzara.
Kamfanin dillancin labaran Mehr, ya ruwaito cewa: Hukumar kare hakkin dan adam ta kasar da ke birnin Sana’a ta sanar da cewa: Hare-haren Saudiyya kan kasar musamman wadanda aka kai kan cibiyoyin ilimi da horon malamai sun kai sama da 2,775 a cikin shekaru 12 da suka gabata.
Hukumar ta kara da cewa: Hare-haren Saudiyya kan makarantu da hasumiyoyin sadarwa sun kara ta’azzara tun daga ranar 3 ga Watan Satumba. Harin da aka kai wa wata makaranta, wadda Saudiyya ta lalata a karo na uku, ya nuna cewa Yemen tana fuskantar wata manufa ta siyasa da ta saba wa ilimi.
Hukumar kare hakkin dan adam ta kasa ta Yemen ta bayyana cewa ta yi Allah wadai da harin da Saudiyya ta kai wa makarantar Al-Rawd da ke Taiz, wanda ya lalata ta gaba daya.
A cikin ‘yan sa’o’in da suka gabata, kamfanin dillancin labarai na Saba da ke birnin Sana’a ya ruwaito cewa: Jiragen saman yakin Saudiyya sun kai hari kan makarantar Al-Rawd da ke gundumar Al-Rabia, arewa maso yammacin Taiz, a karo na uku, inda suka lalata abin da ya rage a makarantar.