Ana ci gaba da yin Allah wadai da tofin Allah tsine kan farmakin da Isra’ila ta kaddamar kan yankin Jenin a yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye.
Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin da sojojin Isra’ila suka kai kan birnin Jenin da ke gabar yammacin kogin Jordan.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta ce: Saudiyya ta sake yin kira ga kasashen duniya da su dauki alhakin dakatar da keta dokokin kasa da kasa da Isra’ila ke yi.
Ma’aikatar ta yi gargadin cewa halin da ake ciki na iya haifar da sake barkewar tashin hankali wanda zai maida hannun ogogo baya ga kokarin samar da zaman lafiya a yankin.
Ita ma Qatar ta yi “kakkausan Allah-wadai da tofin Allah tsine” kan harin da kuma kashe fararen hula a wurin, tana mai bayyana tashin hankalin a matsayin “babban cin zarafi ga dokokin kasa da kasa da hakkin bil adama”.
Ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta kuma yi kira ga kasashen duniya da su “dau nauyin da ya rataya a wuyansu na tunkarar wadannan laifuka, da kuma kokarin tabbatar da cikakken kare fararen hula bisa tanadin dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyoyin da suka dace”.
Sanarwar ta nanata matsayar kasar Qatar na samun damar kafa kasarsu mai cin gashin kanta a kan iyakokin shekarar 1967, tare da gabashin Kudus a matsayin babban birni.