Saudiyya Da Kawayenta Sun Kai Jerin Hare-Hare Kan Yemen

Kakakin Rundunar Sojin Yemen ya bayyana cewa: Jiragen saman yakin Saudiyya sun kai hare-hare da makamai masu linzami 14 kan Yemen cikin awanni 24 da

Kakakin Rundunar Sojin Yemen ya bayyana cewa: Jiragen saman yakin Saudiyya sun kai hare-hare da makamai masu linzami 14 kan Yemen cikin awanni 24 da suka gabata

Kakakin Rundunar Sojin Yemen Yahya Sare’i ya sanar da cewa: Dakarun kawancen da Saudiyya sun jagoranci kai hare-hare ta sama da makamai masu linzami guda 14 a kan kasar Yemen cikin awanni 24 da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran Mehr, ya ruwaito cewa: Yahya Sari’e, kakakin rundunar sojin Yemen, ya sanar da cewa: Jiragen saman Saudiyya sun kai hare-hare ta sama da makamai masu linzami guda 14 a yankuna daban-daban na Yemen a cikin awanni 24 da suka gabata.

Kakakin ya bayyana cewa: an kai hare-haren Saudiyya ne ta hanyar amfani da jiragen sama kirar F-15 da jiragen yaki na Typhoon daga sansanonin jiragen saman Khamis Mushait da Taif, kuma an kai hare-hare da makami mai linzami daga Najran.

A cewar rahoton, Sari’e ya nuna cewa: Hare-haren da aka kai da makamai masu linzami na Saudiyya a cikin awanni 24 da suka gabata sun kai hare-haren ne kan yankunan Taiz, Amran, Marib, da Saada.

Kakakin ya jaddada cewa: Jimillar hare-haren sama da makamai masu linzami da kawancen Saudiyya ke jagoranta tun bayan karuwar tashin hankali ya kai 1,032.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted