Sarkin Qatar Zai Zayarci Tehran A Gobe Laraba

Sarkin Qatar Tamim bin Hamad Al-Thani zai fara ziyarar aiki na kwana guda a nan Tehran, don tattauna al-amura masu muhimmanci da Jami’an gwamnati JMI.

Sarkin Qatar Tamim bin Hamad Al-Thani zai fara ziyarar aiki na kwana guda a nan Tehran, don tattauna al-amura masu muhimmanci da Jami’an gwamnati JMI.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbass Aragchi ya bayyana cewa, a gobe muna tare da sarkin Qatar Tamim bin Hamad Athani, inda zamu tattauna al-amura masu muhimmanci a tsakanin kasashen biyu.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar cewa kasar Qatar ta taka rawa a tsagaita wuta tsakanin HKI da kuma kungiyar Hamas, sannan tana da dangantaka mai karfi da kasar Iran.

Ya ce yankin gabasa ta tsakiya tana fuskantar sauye-sauye masu yawa, da kuma barazana iri-iri, kuma wannan zuwan zai kasance sabonta dangantaka tsakanin kasashen biyu ne.

Duk da cewa Aragchi bai bayyana agendar tattaunawar kasashen biyu ba, amma akwai,  zaton kasashen biyu zasu tattauna kan sauye-sauyen da ke faruwa a gabas ta tsakiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments