Kasar Iran Zata Aika Da Tawaga Mai Karfi Zuwa Jana’izar Sayyid Nasarallah

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’el Baghae ya ce gwamnatin kasar Iran zata aika tawaga mai karfi zuwa kasar Lebanon don halattar Jana’izar Sayyid Hassan Nasarallah wanda za’a gudanar a cikin yan kwanaki masu zuwa. Bakha’I ya kara da cewa,  zamu halarci Jana’izar a kasar Lebanon, kuma zamu aika da tawaka wacce zata kunshi […]

Sarkin Qatar Zai Zayarci Tehran A Gobe Laraba

Sarkin Qatar Tamim bin Hamad Al-Thani zai fara ziyarar aiki na kwana guda a nan Tehran, don tattauna al-amura masu muhimmanci da Jami’an gwamnati JMI. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbass Aragchi ya bayyana cewa, a gobe muna tare da sarkin Qatar Tamim bin Hamad Athani, inda zamu tattauna al-amura masu muhimmanci a tsakanin kasashen […]

Sojojin HKI Sun Fara Ficewa Daga Wasu Wurare A Kudancin Kasar Lebanon

Ministan watsa labarai na kasar Lebanon Mr Paul Marcos ya bada sanarwan cewa sojojin HKI sun fara janyewa daga yankunan da suke mamaye da su a kudancin kasar Lebanon. Wanda kuma zai bada daman ga sojojin kasar su maye gurbinsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana cewa wannan sauyin zai […]

Sojojin HKI Sun Ce Ba Zasu Fita Daga Wurare 5 A Kudancin Kasar Lebanon Ba

taswirar Syria

Sojojin HKI Sun Bada sanarwan cewa ba zasu bar wasu tuddai guda 5 a kudancin kasar Lebanon ba, har zuwa wani lokacin da basu sani ba, saboda tsaron haramtacciyar kasar. Tashar talabijin ta Almayadin ta  kasar Lebanon, ta nakalto cewa tankunan yakin HKI sun kutsa cikin garin kafarshuba na kudancin kasar Lebanon kuma sun kafa […]

IRGC: Za Mu Kai Farmakin “ Wa’adus-Sadik” Na 3 Akan ‘Yan Mamaya

Mataimakin kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran “IRGC” ya sanar da cewa; Iran za ta kai farmakin “Wa’adus-Sadik 3”  a lokacin da ya dace. Laftanar janar Ali Fadwi ya kuma yi ishara da yakin Gaza, yana bayyana cewa, su kansu ‘yan sahayoniya sun bayyana cewa Hamas ta yi nasara, su kuma ba […]

Hamas Ta Sanar Da Shahadar Wani Jagoranta Da HKI Ta Kashe A Lebanon

Dakarun “Kassam” na kungiyar Hamas sun sanar da shahadar Muhammad Shahin wanda daya ne daga cikin kwamandojinta da ya yi shahada sanadiyyar harin da HKI ta kai masa a birnin Saida na kasar Lebanon. Sanarwar ta dakarun “Kassam” ta ce, Muhammad Ibrahim Shahin wanda ake yi wa lakabi da Abul-Bara’a ya yi shahada ne a […]