Sanders Yayi Kira Da A kawo Karshen Yakin Amurka Kan Kasar Iran

fitaccen sanata a kasar Amurka sendars yay kira da a kawo karshen yakin da amurka da isra'ila suka kaddamar kan kasar iran

Sanata mai zaman kasa a kasar Amurka Bernie Sendars yayi tir da yakin da amurka da isra’ila suka kaddamar kan kasar iran da ya sabama doka, yana mai bayyana shi a matsayin yakin da ya ginu  kan yaudara, ya kwatanta wannan yaki da munanan yake yaken da aka yi a viyatnam da iraki, kuma yayi kira da akawo karshen yakin a nan take , a rage kashe kudade sosai a bangaren soji da kuma dakatar da bada tallafin kudi ga gwamnatin mamaya ta isra’ila mai tsaurin kai

Sendars yayi wannan bayani ne a shafinsa na X a jiya Alhamis,inda y ace yakin da aka yi a iraki da viyatnam ya doru ne akan karya, mun kashe kudade masu yawa bangaren soji fiye da kasashe 6 masu zuwa, har yanzu pentagon ba za ta iya bada amsa kan kudade triliyon ba, don haka dole ne a kawo karshen yaki da iran,

Manyan jami’an sojin kasar iran sun tattara bayanai kan kisan fararen hula da amurka da isra’ila suka yi, da ya hada da harin da suka kai kan wata makaranta a kudancin garin Minab inda suka kashe yara 168, matakin da kwamandan dakarun soji kasar iran ya bayyana shi a matsayin laifi da ba za a iya kareshi ba kuma ba za’a amince da shi ba, yace jininsu ba zai tafi haka nan ba tare da mayar da martani ba

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted