Kotun Duniya Ta Yanke Hukuncin Kan Gwamnatin Myanmmar

Kotun duniya ta yanke hukunci kan gwamnatin myanmmar nayin kisan kare dangi kan alummar musulmin rohingya

Babbar kotun duniya mai hukumta laifukan yaki ta ICJ ta yanke hukunci dake tabbatar da cewa gwamnatin Myanmar ta aikata lifin kisan kare dangi kan musulmin Rohingya marasa rinjaye dake arewacin rakhine, kuma ta gano cewa hare haren da sojojin suka kai a shekara ta 2017 an kai su ne da nufin halaka alummar da mafi yawancinsu musulmi ne

A cikin wani hukunci mai tarihi da aka yanke a birnin hugue a jiya alhamis , kotun mai alkalai 15 ta yanke hukunci da kuri’u 9 kan 6 dake tabbatar da cewa kasar Myanmar ta karya yarjejeniyar hana kisan kare dangi ta shekara ta 1948, wannan shi ne karon farko da kotun ICJ ta dora alhakin aikata kisan kare dangi kai tsaye a kan wata kasa

Kotun ta gano cewa jami’an tsaron kasar myanmmar sun kashe dubban fararen hula  yan ruhingya , sun aikata laifukan cin zarafin mata da yara kanana, sanan kuma sun kai hari kan alummar rohingya da suka gudu , kamar yadda alkalin dake jagorantar shari’a ya tabbatar.

Majalisar dinkin duniya ta kiyasta a baya cewa akalla fararen hula yan rohingya 10,000 ne aka kashe a lokacin kisan kare dangi da sojoji suka yi a shekara ta 2017, yayin da sama da miliyan 1 kuma aka korasu zuwa kasar bangaladash, dama daga cikin wadanda suka rage an kashe su ta hanyar keta huruminsu da kuma rusa musu gidaje.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted