Rahotanni sun bayyana cewa Iran ta gargadi Amurka game da kokarin sake dawo da hare haren soji, tana mai bayyana cewa ba za ta kara amincewa da tsawaita yaki ba, ko kuma zama a cikin yanayin da ba yaki, ba zaman lafiya
Kakakin rundunar kare juyin musulunci na iran Brigadier Ganar Hussain mohebi ya bayyana a jiya alhamis cewa iran ta shirya wa duk wani mataki, yana mai jaddada cewa karfin sojan kasar iran ya inganta sosai kuma dakarunta na ci gaba da sanya ido kan motsin sojan Amurka. yace ba zamu taba amincewa da yanayi da ba yaki kuma ba zaman lafiya ba,
Haka zalika ya kara da cewa zamu warware batutuwan da suka shafi yaki baki daya, shi ne ko dai a zabi komawa filin daga ko kuma kasar amurka ta amince da sharuddan da iran ta gindaya
Daga karshe yace abokan aikinmu a rundunar IRGC sun yi aiki ba dare ba rana wajen samar da sabbin tsare-tsare a wannan fanni , ba wai guda daya ba kawai, akalla sama da guda 3, wanda yadda aka inganta tsarin ya wuce bukatun dakarun sojin iran na cikin gida, ana ma fitar da shi zuwa wasu kasashen makwabta, da hakan ke nuna irin ci gaba da kasar ta samu ta fuskar masana’antar tsaro