Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta yi tir da hare haren kisan kare dangi na baya bayan nan da gwamnatin yahudawan sahyuniya ta kai kan yankin gaza , kuma tayi kira ga majalisar dinkin duniya da ta dauki matakin gaggawa domin kawo karshen kisan kare dangi da kuma hukumta wadanda suka aikata mummunan aikin
Haka zalika tayi Allah wadai da laifukan da gwamnatin mamaya ke tafkawa da kuma hare haren ta’adanci da yahudawa yan share wuri zauna ke kai wa kan falasdinawa a yammacin kogin jodan da aka mamaye, cikin har da sabon harin kona masallacin al-ihsan
Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta bayyana cewa rashin daukar matakin amurka da magoya bayan gwamantin mamayar isra’ila suka tilastawa cibiyoyin kasa da kasa , ya kara bai wa gwamnatin karfin guiwa, wanda hakan ya bata damar ci gaba da take hakkin dan adam a yankin falasdinu da take mamaye da shi
Daga karshe ya jaddada cewa dukkan bangarorin da ke da hannu wajen yarjejeniyar da aka cimma a ranar 10 ga watan oktoban shekara ta 2025 a sharm El-shaikh suke da alhakin ganin sun tabbatar da kawo karshen cin zarafin alummar falasdinu da isra’ila ke yi