Schumer Ya Bukaci A Sauke Ministan Yaki Na Amurka

matsaloli sun sa wani dan majalisar amurka ya bukaci a sauke ministan yaki daga mukaminsa

Shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin Amurka Chuck schumer ya bukaci a sauke ministan yakin Amurka pete hegseth cikin gaggawa saboda da rashin cancantarsa,  yace lokacin da ma’aikatan jirgin ruwan Amurka ke fuskantar mummunan yanayi a cikin jirgin ruwan Uss Abraham Lincoln a lokacin da Washington ke ci gaba da kai wa iran hari

A cikin wani bayani da ya wallafa a shafinsa na X a jiya alhamis Schumer ya ce lokacin da aka zabi Hegseth kowa yasan cewa bai cancanta ba, amma yanzu dakarunmu sune ke biya farashi ta hanyar mafi muni, don haka wajibi ne hegseth ya sauka daga kan mukaminsa

Wannan yana zuwa ne adaidai lokacin da ake aiko da rahotanni dake nuna irin mawuyacin hali da ma’aikatan jirgin ruwa da sojoji  guda 5000 ke ciki, a jirgin ruwa mai amfani da makamashin nukiliya, wanda ya shafe sama  da kwanaki 250 yana cikin tekun tun bayan barinsa san Diego a watan nuwamba shekara ta 2025 da ta gabata

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted