Salami : Gazawar Isra’ila A Lebanon Ne Ya Tilasta Mata Tsagaita Wuta

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Hossein Salami ya mika sakon taya murna ga babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Hossein Salami ya mika sakon taya murna ga babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naeem Qassem bisa gagarumar nasara da kungiyar Hizbullah ta samu wajen dakile manufofin Isra’ila a fagen arewacin kasar da kuma tilastawa tsagaita wuta.

A cikin bayaninsa Janar Salami ya bayyana gazawar gwamnatin Isra’ila wajen cimma manyan manufofinta a arangamar ta baya-bayan nan, yana mai kiran tsagaita bude wuta a matsayin wani abin kunya ga Tel Aviv.

A cikin sakon da ya aike wa Sheikh Naim Qassem, babban hafsan IRGC ya yaba da juriyar al’ummar kasar Labanon, sadaukarwar da mayakan Hizbullah suka yi. Y

Ya bayyana nasarar a matsayin wani lokaci mai ma’ana a tarihin gwagwarmaya da ‘ya sahayoniya a fadin yammacin Asiya.

“Ba shakka, wannan babbar nasara da aka samu ta hanyar tsarkakakken jinin shahidai, da hakurin al’ummar kasar Labanon, da jarumtakar mayakan Hizbullah da ba a taba ganin irinsa ba—wani lamari ne mai girma a tarihin tsayin daka.

Daga karshe ya jaddada goyon bayan Iran ga kungiyoyin gwagwarmayar Musulunci a Falastinu da Lebanon, yana mai cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen yakar Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments