Search
Close this search box.

Sakon Jagora Ga Mahajjata Na shekara Ta 2024

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su kara tabbata ga fiyayyen halitta, shugabanmu

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su kara tabbata ga fiyayyen halitta, shugabanmu Annabi Muhammadu al-Mustafa, da alayensa tsarkaka, da sahabbansa zababbu da wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

Wannan kira na Annabi Ibrahim mai jan hankali, wanda bisa ga umarnin Allah ya yi kira ga dukkan bil’adama a kowane zamani zuwa dakin Ka’aba a lokacin aikin Hajji, ya sake janyo hankulan dimbin al’ummar musulmi daga sassan duniya zuwa wannan cibiya ta tauhidi da hadin kai.

Ita ce ta haifar da wannan gagarumin taro mai ban sha’awa na ɗimbin jama’a, wanda ke bayyana yanayin ɗan adam da karfin ruhin Musulunci ga kansa da kuma ga wasu.

Idan mutum ya yi la’akari da wannan gagarumin taro da hadaddiyar ibadar Hajji, su ne abin da zai sanyaya zuciya da kuma kara kwarin gwiwa ga musulmi, tare da zama abin tsoratarwa da firgici ga makiya da masu mugun nufi a kan musulunci.

Bai kamata ya zo da mamaki ba idan makiya da masu mugun nufi a kan  al’ummar musulmi suka yi yunkurin ruguzawa da sanya shakku a kan wadannan bangarori biyu na aikin Hajji – walau ta hanyar jaddada banbance-banbancen mazhabobi, da batutuwa na siyasa, ko kuma ta kokarin rage muhimmanci. na bangarorin hajji masu tsarki da karfafa ruhi.

Kur’ani ya gabatar da aikin Hajji a matsayin bayyananniyar ibada, zikiri [ambaton Allah], tawali’u da kuma daidaiton darajar dukkan bil’adama. [Yana gabatar da aikin Hajji a matsayin] bayyanar tsarin rayuwar dan’adam a duniyance da kuma ta fuskar ruhi, bayyanar albarka da shiriya, da bayyanar da aminci da zaman lafiya tsakanin ‘yan’uwa [na addini] a aikace. Kuma [kur’ani ya gabatar da aikin Hajji a matsayin bayyanar da karfi da daukakar al’ummar musulmi a kan makiya.

Idan aka yi la’akari da ayoyin da suka shafi aikin Hajji da yin la’akari da ayyukan ibada na wannan aikin farilla da ba su misaltuwa, ya bayyana wadannan al’amura da sirruka da makamantansu, kamar yadda wadannan abubuwa ke nuni abubuwa masu sarkakkiya da wahala da ke tattare da aikin Hajji.

‘Yan’uwa, a matsayinku na mahajjata masu gudanar da aikin Hajji, a halin yanzu kuna wurin da za ku iya aiwatar da wadannan abubuwa da aiki yake koyarwa masu cike da haske. Ku kusantar da tunaninku da ayyukanku kusa da wadannan abubuwa, kuma ku dawo gidajenku da abin da ke tattare da wadannan abubuwan da kuka koya masu madaukain matsayi na kololuwa . Wannan shi ne muhimmin abin tunawa na tafiyar ku aikin Hajji.

A wannan shekarar, lamarin bara’a ya fi kowane lokaci muhimmanci. Masifun da ke faruwa a Gaza, wadanda ba su da abin misaltawa a tarihinmu na wannan zamani, tare da jajircewar gwamnatin sahyoniya maras tausayi, wanda ke nuni da zalunci da muguwar dabi’a, duk da cewa wannan bai bar wani shakku ga wani mutum, ko wata jam’iyya ko gwamnati ko wani bangare na al’ummar ba, kan tabbacin gushewar gwamnatin sahyuniya.

Dole ne al’ummomi da gwamnatoci su ci gaba da nuna bara’a ga gwamnatin sahyuniya da masu mara mata baya musamman Amurka a zantuka da kuma aikace, tare da dakile ayyukan azzalumai makasa.

Gwagwarmaya mai karfi ta Falasdinu da mutane masu haƙuri, mutanen Gaza da ake zalunta,  wadanda hakurinsu na ban mamaki da tsayin daka ya zama mai da girmamawa a duniya,  dole ne a ba su cikakken goyon baya ta kowace hanya.

Ina rokon Allah Ya ba su cikakkiyar nasara a cikin gaggawa. Kuma gareku alhazai ina yi muku addu’ar Allah ya karbi aikin Hajjin ku. Allah ya karfafe ku da addu’ar Baqiyatullah (Imam Mahdi AS).

Aminci ya tabbata a gare ku da rahmar Allah

Sayyid Ali Khamenei

Dhu al-Hijjah 4, 1445

Yuni  11, 2024

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments