Sakataren Majalisar Tsaron Kasar Iran Ya Gana Da Vladmir Putin Na Kasar Rasha

Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijai ya isa birnin Moscow inda ya gana da shugaban kasar Rasha Valdmir Putin. Fadar mulkin

Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijai ya isa birnin Moscow inda ya gana da shugaban kasar Rasha Valdmir Putin.

Fadar mulkin kasar Rasha “Kremlin” ce ta sanar da cewa an yi ganawar ne akan abubuwan da suke faruwa a cikin wannan yankin da kuma alakar kasashen biyu.

Su ma kafafen watsa labarun kasar Rasha sun ce ganawar da Dr.Larijani da shugaban kasar Vladmir an yi ta ne adaidai lokacin da wannan yankin yake cikin wani yanayi mai matukar hatsari, da kuma barazanar da Amurka take yi. Haka nan kuma kafafen watsa labarun sun ce; bangarorin biyu sun kuma tattauna hanyoyin aiki tare ta fuskokin soja da kuma tsaro.

A wani labarin mai alaka da sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran,Dr. Ali Larijani ya gargadi kungiyar tararyyar turai akan daukar dakarun kare juyin musulinci ( i.r.g.c) da ta yi a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.

Kamfanin dillancin labaran ISANA na kasar Iran ya nakalto Dr Ali Larijani sakatarin majalisar koli ta tsaron kasar Iran yana fadar haka. Dr Larijani ya kara da cewa  wasu kasashen da suke kiran dakarun kare juyin juya halin muslunci a matsayin  ‘yan ta’adda, a wajen Iran su ne yan ta’adda na gaskiya,kuma snnan a hankali za su girbi abinda suka shuka da wannan matakin da suka dauka a kan IRGC.

Larijani ya bayyana haka ne a jiya Jumma’a a shafinsa na zumunta na X, a lokacinda yake mayar da martani ga kasashen turai kan matakin da suka dauka a kan dakarun na IRGC.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted