Gwamnatin Iran ta nada Fatimah Mohajerani a matsayin mai magana da yawun gwamnatin kasar
Sabuwar gwamnatin Iran bisa shawarar shugaban kasar Masoud Pezeshkian ta sanar nada Fatimah Mohajerani a matsayin mai magana da yawunta.
Gwamnatin Iran ta 14 ta nada Fatimah Mohajerani a matsayin kakakinta da Kamel Taqawi a matsayin sakataren majalisar gwamnatin kasar bisa shawarar da shugaban kasar Masoud Pezeshkian ya gabatar bayan wadannan mukamai guda biyu Ali Bahadori Jahromi ne ya rike su a gwamnatin Iran ta 13.
Abin lura shi ne cewa: An haifi Fatima Mohajerani ce a birnin Arak da ke tsakiyar kasar Iran a shekara ta 1970. Kuma ta jagoranci jami’ar fasaha ta Shari’a da koyar da sana’o’i ga mata a gwamnati ta goma sha daya, kuma ministan ilimi na wancan lokacin Muhammad Badaha’i ya nada ta shugabar Cibiyar Hazaka a ranar 18 ga Oktoban shekara ta 2017.