Sabbin Hare-Hare A Gaza Sun Kashe Falasdinawa Akalla 25

A dai dai lokacinda rashin abinci, ko yuwan take kara tsanani a gaza, HKI tana ci gaba da kissan Falasdinawa a Gaza, inda a safiyar

A dai dai lokacinda rashin abinci, ko yuwan take kara tsanani a gaza, HKI tana ci gaba da kissan Falasdinawa a Gaza, inda a safiyar yau Asabar sojojin HKI suka kashe falasdinwa akalla 25 a wuraren karban abincin taimako.

Shafin yanar gizo na labarai ‘Arab News’ ya bayyana cewa hakan na faruwa ne a dai-dai lokacinda MDD ta yi gargadin cewa yunwa ta bayyana Gaza.

Labarin ya kara da cewa watanni 22 da suka gabata kenen da fara yaki a Gaza, sojojin HKI sun kashe Falasdinawa fiye da falasdinawa 62000.

Sannan yunwa ta kashe Falasdinawa kimani 1000 mafi yawansu yara kanana ko jarirai. A halin da ake ciki a yanzun dai gwamnatin Natanyahu ta sha alawashin kwace zirin Gaza gaba daya daga hannun kungiyar Hamas, sannan zata bar sauran Falasdinawa su fice daga yankin idan suna bukata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments