Kwamandan rundunar ‘yan sandan Iran ya jaddada cewa: Duk wani hari daga abokan gaba za a mayar da martani mai karfi
Babban Kwamandan Rundunar Tsaron Iran na ‘Yan Sanda ya tabbatar da cewa: Matakan Tsaro suna aiki a matsayin abin koyi na kare kasa, wanzar da zaman lafiya da kuma aminci, yana mai jaddada shirin rundunar ‘yan sanda na fuskantar kowace barazana.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Mehr, Birgediya Janar Ahmad Reza Radan, Babban Kwamandan Rundunar Tsaron na ‘yan sandan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya fitar da sako a lokacin fara Makon Tsaro cewa: Makon Tsaron Tsarki yana wakiltar kololuwar sadaukarwa da kuma bayyanar ƙarfin da jurewa na al’umma da ya samo asali daga matakan Imani da ruhin kalubalantar rashin imanin masu girman kai, da kuma kokarin dakile lissafinsu na neman aiwatar da mulkin mallaka.
Janar Ahmad Reza Radan ya jaddada cewa: A yau, yayin da suke sake fuskantar ƙalubalen masu girman kai na duniya, Tsaron Tsarki ba wai kawai wani lamari ne na tarihi a gare su ba, amma a maimakon haka koyarwar aiki da kuma samfurin juriya da karfin ruhi ne gare su. A baya sun sami damar karya makircin gwamnatin Ba’ath duk da Rashin isassun makaman yaki, tare da ƙarancin ƙarfin soja, don haka a halin yanzu da Allah ya azurta su da kayan yaki zasu dukufa wajen kalubalatar makiya.