Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da kashe gawurtaccen dan bindigan nan, Aminu Kanawa wanda shi ne mataimakin Bello Turji.
Sojojin Operation Fansan Yamma ne suka kashe Aminu a wani samame da suka kai tsakanin ranakun 20 zuwa 21 ga Janairun 2025.
Kashe Aminu Kanawa na zuwa ne kasa da mako guda bayan sojojin na Operation Fansan Yamma sun kashe dan Bello Turji a wani samame da sojojin suka kai a Fakai.