Kafofin yada labaran Isra’ila sun bayar da rahoton a wannan Alhamis cewa, sojojin mamaya na Isra’ila sun sanar da mutuwar wani soja guda tare da jikkatar wani a cikin sa’o’i 24 da suka gabata a yankin arewaci da ke kan iyakar Lebanon da Falasdinu da yahudawa suka mamaye.
Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da cewa an kashe sojan na Bataliya ta 5030 na Alon Brigade a lokacin da suke fafatawa da dakarun kungiyar Hizbullah a kudancin kasar Lebanon, yayin da wani sojan kuma ya samu munanan raunuka a wannan artabu, kuma tuni aka garzaya da shi zuwa asibiti, a cewar bayanin rundunar.
A bisa ikirarin rundunar sojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila, adadin sojojinta da suka hakala a karon battarsu da Hizbullah aa kan iyaka da Lebanon ya kai sojoji 12, duk da cewa abbu wasu sahihan bayanai da suke iya tabbatar da wanann ikirari.
Kafofin yada labaran Isra’ila sun bayar da rahoton a ranar Laraba cewa sojojin mamaya na Isra’ila sun sanar da jikkatar sojojinsu 38 a kan iyakar Lebanon da Falasdinu da ta mamaye.
A kasa, kungiyar gwagwarmayar Musulunci a kasar Lebanon – Hezbollah ta yi nasarar dakile yunkurin kutsawa da dama daga sojojin mamaya na Isra’ila a wurare daban-daban a kudancin Lebanon tun da sanyin safiyar Talata har zuwa yau, sanann kuma kungiyar Hizbullah ta tabbatar da cewa adadin sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila da suka halaka a lokacin yunkurin kutsawa cikin kasar Lebabon suna da yawa, amma Isra’ila tana boye yawan adadin sojojinta da suka hakala a karawarsu da dakarun Hizbullah.