Rundunar “IRGC”: Koran Amurka Daga Iraki Babban ‘Yanci Ne

Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta bayyana cewa: Korar Amurka daga kasar Iraki wani shiri ne na ‘yantar da Yammacin Asiya daga karkashin Babban

Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta bayyana cewa: Korar Amurka daga kasar Iraki wani shiri ne na ‘yantar da Yammacin Asiya daga karkashin Babban Shaidan

Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta (IRGC) ta fitar da sanarwa game da janye sojojin Amurka daga Kasar Iraki cewa:

Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta “IRGC”, wajen tunawa da shahidan Kare Juyin Juya Halin Musulunci a Iraki da Yammacin Asiya, musamman Janar Qassem Soleimani da ya yi shahada da Abu Mahdi al-Muhandis, da kuma dukkan mujahidai da suka samu girman shahada a tsawon shekaru ashirin na fafatawa da Amurkawa, suna taya jarumtakar mutanen Iraki, kungiyar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci mai alaka da mujahidan juyin juya halin Musulunci a duk fadin duniya  murna kan wannan nasara mai tarihi.

Korar Amurka daga Iraki sakamakon juriya da jarumtakar mutanen wannan kasar wajen kare ‘yancinsu. Ta hanyar juriyarsu ta tarihi, mutanen Iraki sun tabbatar da cewa kudurin kasa shine makamin karshe da zai yaki burin masu girman kai. Nasarar juriyar kin jinin mulkin mallaka a Iraki mai alfahari da kin mamayar Amurka shi ne zinare a tarihin ‘yantar da al’ummar yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted