Kakakin Rundunar Tsaro Juyin Juya Halin Musulunci ya jaddada cewa: Dole ne a samu kwakkwaran haɗin kai tsakanin sojoji da Rundunar tsaron Juyin Juya Hali a tsawon tarihi
Kakakin Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta (IRGC), Birgediya Janar Hussein Mohebi, ya bayyana cewa: Hadin kan da ke tsakanin sojoji da rundunar IRGC ya kamata a rubuta shi a tsawon tarihi kuma a tabbatar da shi a kowane bangaren tarihin kasa.. Ya kara da cewa: “Sojojin Iran abin alfahari ne ga Kasar ta Musulunci, kuma wata cibiya ce mai karfi da shahara da ke kare kasarta daga abokan gaba.”
Kamfanin dillancin labaran “IRNA” na Iran ta ruwaito cewa: Birgediya Janar Mohebi ya gana da kakakin rundunar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Birgediya Janar Mohammad Akrami Nia, a hedikwatar rundunar. Sun tattauna hanyoyin karfafa hadin gwiwa da hadin kai tsakanin rundunar sojojin da rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta IRGC, da kuma yadda za a ci gaba da bunkasa martabar rundunar sojojin a gaban abokan gaba.