Kakakin rundunar sojin Al-Qassam ya ce: Wani mafarki mai ban tsoro yana jiran ‘yan sahayoniyya daga jaruman al’ummar Falasdinu
Kakakin rundunar sojin Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, Abu Ubaida, ya jinjinawa aikin jarumtaka da aka gudanar a mashigar Karama da Jarumin shahidan kasar Jordan (Mahir Al-Jazi), daya daga cikin jaruman Ambaliyar Al-Aqsa ya kai.
Abu Ubaida ya yi nuni da cewa: Bindigar da jarumin Jordan ya yi amfani da ita wajen kare kimar Masallacin Aksa da al’ummar Falasdinu ta fi tasiri a kan dimbin sojoji da kuma rumbun makaman sojan makiya ‘yan mamaya.
Ya yi nuni da cewa: Wannan hari yana bayyana karfin ruhin al’umma ‘yan gwagwarmaya ne da sakamakon tasirin da harin Ambaliyar Al-Aqsa ta haifar gami da tabbatar da mummunan mafarkin da ke jiran yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya daga jaruman al’ummar Musulmi.
Wannan matashi dan kasar Jordan mai suna Mahir Al-Jazi ya kai farmakin kwamandoji ne a jiya Lahadi a mashigar Karama dake tsakanin Jordan da Falasdinu da aka mamaye, inda ya yi sanadin kashe wasu yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida guda 3 tare da jikkata wasu 3 na daban kafin ya kai ga yin shahada. Wannan farmakin dai ya haifar da firgici da rudanin tsaro a cikin hukumar yahudawan sahayoniyya, lamarin da ya janyo tunatar da jerin ayyukan jarumtaka da ‘yan kasar Jordan suka kai a baya kan ‘yan mamayar yahudawan sahayoniyya.