Rikicin cikin gida dana diflomasiyya waje sun yi wa Habasha Katutu

rikici ya kara kamara tsakanin habasha da makwabtanta kamar masar sudan da eretiriya

Fada ya ci gaba da rincabewa a arewacin Habasha inda alƙaluma ke nuna cewa daruruwa sun mutu yayinda wasu dubbai suka jikkata, a wani yanayi da rikicin cikin gida dana diflomasiyya ke ƙoƙarin yiwa gwamnatin shugaba Abiy Ahmed rubdugu, bayan da ƙasar ta yanke hulɗar diflomasiyya da maƙwabciyarta Eritrea baya ga korar jami’an Masar kodayake tuni Alƙahira ta mayar da martani.

Masar ta baiwa babban jami’in diflomasiyyar Habasha sa’o’i 48 ya bar ƙasar kwana guda bayan Addis Ababa ta koro nata jami’I, dai dai lokacin da tankiya ke ƙara zafafa tsakanin Habasha da maƙwabtanta, musamman Eritrea da Sudan da kuma Masar, waɗanda a baya-bayan nan ta zargi ta da hannu wajen tunzura mayaƙan ƴan tawayen TPLF.

Tun gabanin yaƙin na ƴan tawayen Tigray da gwamnatin ta Habasha da ke ƙoƙarin dawowa sabo, rigimar da ke tsakanin Masar da Habashan ta faro ne tun daga ginin madatsar ruwan da Firaminista Abiy Ahmed ya yi a kan tekun Nilu, yayinda Khartoum kuma ta zarge ta da goyon bayan mayaƙan RSF da ke yaƙi da dakarun gwamnati fiye da shekaru 3.

A gefe guda Eritrea wadda ta taimakawa Habasha yaƙar ƴan tawayen a baya, tun bayan kawo ƙarshen yaƙin a 2022 ne rikici ya tsananta a tsakaninsu, yayinda a yanzu Addis Ababa ke zargin Asmara da taimakon ƴan tawayen a yanzu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted