Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran ya mayar da martani ga kalaman Trump na baya-bayan nan
Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran Manjo Janar Mohsen Reza’i, ya bayyana cewa: Iran ita ce ke samar da gaskiya, tare da mutanenta, sojojinta da kuma makamai masu linzami.
A cikin wani rubutu da ya yi a dandalin X, a matsayin mayar da martani ga maganganun rudu na shugaban Amurka Donald Trump na kawo karshen yaki: Rezaei ya rubuta cewa: “Bayan shan kaye a jere, shugaban ƙasa mafi muni a tarihin Amurka yana ci gaba da surutu ba kakkautawa, har ma kalaman nasa sun wuce iyakar rudu da hasashen na kansa. Mutum na iya samun nasara a kowace rana a duniyar hasashe, amma Iran ce ke tsara zahirin gaskiya—tare da al’ummarta, sojojinta, da kuma makamai masu linzami nata.