A lokacin ganawar tasu da majo janaral muhsen reza’I , jagoran juyin musulunci na kasar Iran Ayatollah sayyid mujtaba khamena’I ya jaddada muhimmancin amincewa da dukkan sharudan iran kafin kawo karshen yakin da amurka ta kaddamar akanta
Haka zalika jagoran juyin musulunci na iran ya bayyana cewa ficewar da makiya sukayi sakamakon juriya da alummar iran suka nuna ne, ya kuma jaddada bukatar yin Magana da jama’a cikin lokaci don ci gaba da shiga cikin harkokin kare kasa da kuma tsarin siyasa na kasar
Anasa bangaren major janaral muhsin rezai ya gabatar da rahoto game da yanayin da ake ci a bangarorin daban daban da suka shafi iran, yace daga cikin muhimman mataken da ake dauka a majalisar koli ta tsaron kasa shi ne ciyar da mataken jamhuriyar musulunci gaba, wanda ke nufin kafa tsare-tsaren yaki da suka samo asali daga cikin yankin da kansu,
kasar Amurka da isra’ila sun yi laifukan yaki kan kasar iran na farko wanda ya dauki kwanaki 12 a watan yuni shekara ta 2025 sai kuma na biyu inda ta kaddamar da yaki da ya fara a ranar 28 ga watan fabareru na shekara ta 2026 wanda daga bisani a aka dakatar da shi na wucin gadi a farkon watan aprilu bayan kwashe kwanaki 40,
Sai dai dukkan guda biyun iran ta nuna turjiya da kuma maiyar da martani mai tsanani da ya tilastawa makiya amincewa da dakatar da bude wuta da komawa teburin tattaunawa