Rezaei : Duk Alkawuran Tsaro Na Amurka A Yankin Sun Gaza

"Dole ne tsaro a Yammacin Asiya ya kasance mai tushe daga cikin yankin inji Iran.

Sakataren Majliasar koli ta tsaron kasa na Iran ya bayyana cewa, abin da Amurka ke kira alkawuran tsaro bai amfani ko daya daga cikin kasashen da suka amince da alkawuran Washington din ba.

Manjo Janar Mohsen Rezaei ya ce “alkawuran” da Amurka ta bayar game da tsaron yankin ba su amfani ko daya daga cikin kasashen yankin ba.

“Amurka ta gaza samar da tsaro ga ko daya daga cikin kasashen yankin, kuma rashin tasirin alkawuran tsaro na Washington ya bayyana karara,” in ji Sakataren Majalisar Koli ta Tsaron Kasa ta Iran, Manjo Janar Mohsen Rezaei, a cikin wani sako da ya wallafa da harshen Larabci a shafin X ranar Talata.

“Dole ne tsaro a Yammacin Asiya ya kasance mai tushe daga cikin yankin, kuma dole ne a hana duk wani nau’i na tsoma bakin kasashen waje,” in ji shi.

Kalaman na Rezaei sun zo ne kwana guda bayan ya karbi bakuncin taron tsaro na Tehran, wanda ya hada manyan jami’ai daga kasahen Saudiyya, Turkiyya, da Pakistan.

Jami’an Iran sun yaba da wannan ci gaba a matsayin mataki mai kyau na inganta hadin gwiwa a yankin.

A daya bangaren kuma, Alaeddin Boroujerdi, mamba a Kwamitin Tsaron Kasa da Manufofin Kasashen Waje na Majalisar Dokokin Iran, ya bayyana cewa kasashen yankin sun rasa garanti na Washington na tabbatar da tsaron su, kuma a yanzu suna sake duba manufofinsu.

Dan majalisar ya bukaci gwamnatocin yankunan da su fahimci cewa “Amurka ba za ta iya taimaka musu wajen samar da tsaron su ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted