A jiya ranar farko ta watan Janairu 2026 bayan tsaiko tun zamanin Tarayyar Soviet shu’umin Radiyon ya sake dawowa aiki ta hanyar aikew da sakwanni masu daure kai.
An kafa Rediyon ne a tsakiyar shekarun 1970’s a karnin da ya shude a karkashin wani shiri na ‘ ko-ta-kwana’,ana kuma daukar shi a matsayin wani bangare na aika sakwanin sirri na sojan Rasha.
Daga lokaci zuwa lokaci sautin gurnanin Rediyon yana tsayawa, ya fitar da wani sako da ba a san ma’anarsa ba. A cikin mintoci 20 da aka shiga sabuwar shekarar bana 2026, an ji Rediyon yana fadin wata kalma da harshen Rasha wacce take nufin: “ Hadiyawa” har sau uku, lamarin da masu sharhi ke cewa, watakila yana nufin Rasha za ta hadiye da lakume kasar Ukiraniya,musamman mai dai bayan kwanaki kadan da aka sanar da cewa; Ukiraniya ta kai hari akan masaukin shugaba Vladmir Putin.
A 1991 wannan Rediyon ya watsa Gurnani jim kadan bayan juyin mulkin da bai yi nasara ba akan Shugaban Kasar Soviet na karshe Mikha’il Gorbachov. Haka nan kuma an ji sauyin Rediyon a lokacin mutuwar shugaban Tarayyar Soviet Leonid Brezhnev a 1982.