Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan yayi tattaunawa ta wayar tarho da shugaban kasar rasha vladmir putin inda dukkan bangarorin biyu suka nuna sha’awarsu na kara fadada dangantakarsu da kuma yin aiki tare
A tattaunawar ta su ta wayar tarho, shugaban rasha, putin ya jinjinawa kasar iran game da tsayin dakar da ta nuna wajen tunkarar barazanar Amurka da isra’ila,
Shuwagabanni biyu sun jaddada matsayinsu na kara fadada dangantakartar dake tsakanin kasashen biyu, kuma za ta ci gaba da zama daram ba tare da wata girgiza ba, kuma za su ci gaba da karfafata duk da irin matsalar tsaro da ake fuskanta da kuma rikicin da yake wakana a yankin.
Daga karshe shugaban kasar Rasha ya bukaci shugaban kasar iran ya isar da sakon girmamawa da kuma kyakkyawan fata da jagoran juyin musulunci na kasar iran Ayatollah Sayyed Mojtaba Khamena’I ,kana ya jaddada game da muhimmanci ci gaba da kare dangantakar dake tsakanin Tehran da kuma Moscow.