Rasha: Zelensky Ya Kai Wa Jirgin Ruwan Iran Hari Ne Saboda Ya Sami Karin Kudade

Jami'in diplomasiyyar kasar ta Rasha Rodion Miroshnik ya kuma ce; Furucin da ya fito daga Vladimir Zelensky na cewa Iran tana a matsayin barazana ga
jakadan Rasha Na Musamman

 Jami’in diplomasiyyar kasar Rasha Rodion Miroshnik, yace; shugaban kasar Ukraine Vladimir Zelensky ta tsoma baki a cikin yaki da Iran ne domin ya tallata kansa ga turai ya sami karn kudade.

Jami’in diplomasiyyar kasar ta Rasha Rodion Miroshnik  ya kuma ce; Furucin da ya fito daga Vladimir Zelensky na cewa Iran tana a matsayin barazana ga Ukirain manufarsa samun Karin kudade daga kasashen turai.

Haka nan kuma jami’in diplomasiyyar ta kasar Rasha ya ce; Abinda Vladimir Zelensky yake fada wa turai shi ne; Iraniyawa za su kawo mana hari, don haka ku karo kudi.”

Kasar Ukiraine ta kai wa jirgin ruwan Iran na kasuwanci hari akan doron ruwan tekun “Caspian” wanda ya yi sanadiyyar shahadar daya daga cikin ma’aikatansa.

Iran ta sha alwashin  mayar da martani akan harin

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted