Tashin bom ya kashe wani babban soja a kusa da barikin sojojin kasar Rasha ta ke birnin Mosco a jiya.
Jaridar na National ta kasar Amurka ta bayyana cewa Damir Davydov yam utu bayan da wani bom da aka makalawa mutarsa samfurin BMW ya tashi da shi ya kuma kashe nan take, a kusa da barikin sojojin mai suna Balashikha a wajen birnin Mosco kilomita kimani 14 kacal daga fadar Krimlin.
Davdov mai mukamin kanar shi ne shugaban rundunar sojojin Rasha mai kula da makamai masu linzami da kuma makaman igwa, a rundunar sojojin Rasha, kuma gwamnatin Ukrain tana ganin shi ne, da alhakin mikawa sojojin Rasha makamai da suke kashe yan Ukraine da su.
Kafafen yada labarai ta shafukan Telegaram a kasar Rasha sun bayyana cewa Davdov, dan shekara 57 a duniya ya mutu jim kadan bayan tashin bom din wanda ake zaton hukumar leken asiri na Ukraine ne suka dana shi.